✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ganduje ya yarda a yi sallar Idi da ta Juma’a a Kano

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yarda a yi sallar Idi bayan ya cimma daidaito da malamai da limaman jihar a kan matakan kariya…

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yarda a yi sallar Idi bayan ya cimma daidaito da malamai da limaman jihar a kan matakan kariya daga kamuwa da cutar COVID-19 a lokacin sallolin.

Gwamna Ganduje ya sanar da haka ne ranar Litinin bayan taron da ya yi da malaman addinin Musulumci a Gidan Gwamnati da ke Kano.

“Gwmanati ta duba yiwuwar ba da damar yin sallar Idi a daukacin masarautu biyar na jihar Kano bisa kiyaye matakan kariya”, inji shi.

Haka zalika gwamnan ya ce za a yi sallar Juma’a wadda ita ma aka hana a tsawon makwanni a jihar, yana bayyana cewa ‘yan Hisba za su yi aikin sanya ido domin tabbatar da masallatai na bin ka’idojin kariya a lokacin sallar.

Gwamnan ya bayyana cewa za a sassauta dokar kulle a jihar  sau uku a mako, a ranakun Litinin, da Laraba, da Juma’a, kuma  mazauna jihar za su samu damar walwala ne daga karfe 10 na safe zuwa 6 na yamma.

“A kan haka ne muka bai wa hukumar Hisba umarni ta yi zama da limamai sannan ta tura jami’anta a daukacin masallatan Juma’a na jihar Kano domin su tabbatar ana bin matakan kariya da suka hada da bayar  da tazara da  juna, wanke hannu da kuma amfani da man tsaftace hannu na sanitiser“, inji Gwamna Ganduje.

Ba hawan sallah

Bugu da kari gwamnan ya ce ba za a yi bukukuwan sallah ba, ciki har da hawan sallah, a daukacin masarautun jihar biyar.

“Sai dai ba za a yi bukukuwan salla ba a daukacin masarautu, haka zalika babu hawan salla,” inji shi.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da yin aiki tukuru domin ganin an samu hadin gwiwa wajen yaki da annobar coronavirus a jihar.

Wannan mataki da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya dauka na zuwa ne jim kadan bayan da gwamnatin tarayya ta tsawaita dokar kulle da makwanni biyu a jihar.