Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan mutum 18 da suka rasu a sakamakon ambaliyar ruwa a Doguwa, inda ya ba wa kowannensu kyautar Naira 200,000.
Mamatan su 18 fasinjoji ne da motarsu ta yi hatsari bayan ruftawar wata gada a sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya.
- Yadda karyewar gada ta kashe mutum 18 a Kano
- Akwa United ta lashe Firimiyar Najeriya karon farko a tarihi
A addu’arsa ga muanen da a ambaliyar ruwan wanda shi ne mafi muni tun bayan faduwar damina a bana, Ganduje ya ce, “Mun kadu matuka da samun labarin. Muna rokon Allah Ya gafarta musu, Ya karbi shahadaru tunda ruwa ne ya yi ajalinsu. Allah Ya yi musu rahama Ya sa Aljanna Firdausi ta zama makomarsu, amin”.
Iyalan wadanda abin ya rutsa da su sun yi godiya ga gwamnan game da karimcin da ya nuna musu tare da addu’ar samun nasarar kammala mulkinsa a 2023.
Wadanda abin ya rutsa da su sun fito ne daga garin Doguwa na Karamar Hukumar Doguwa a Jihar, wadda take da nisan kilomita 200 daga birnin Kano.
Gwamna Ganduje ya samu rakiyar da Dan Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa da shugabannin jam’iyyar APC da dattijai da kwamishinoni da mambobin Majalisar Zartarwa ta Jihar da hadimansa da sauran manyan ma’aikatan gwamnati.