Mai ba Gwamnan Kano Shawara kan Kafafen Watsa Labarai, Salihu Tanko Yakasai ya bayyana Gwamna Ganduje a matsayin jagoran yaki da cin hanci da rashawa a fadin Nijeriya.
Salihu Tanko Yakasai a tattaunawarsa da Aminiya ya kafa hujja da wasu dalilai uku, a ikirarin nasa kan gwamnan da a shekarun baya ake zarginsa da karbar kafin alkalamin daloli daga hannun ’yan kwangila bayan bullar wani bidiyo da ya jawo ce-ce-ku-ce.
“Na farko dai, Kano ita ce jiha daya tilo da ke da hukuma mai zaman kanta da ke yaki da cin hanci da rashawa a duk fadin Nijeriya, kamar yadda ake da hukumar EFCC a matakin kasa.
“A nan ne talakawa ke kai kokensu a kuma bibiyi korafe-kirefensu a kwato musu hakkokinsu.
- Ganduje ya dawo da Salihu Tanko bakin aikinsa
- Gwamnatin Kano ta yi barazanar soke zangon karatu na uku
- Sabon Sarkin Zazzau ya kai ziyara Masarautar Kano
Salihu Tanko Yakasai dai shi ne wanda a larabar nan Ganduje ya dawo da shi bakin aikinsa bayan dakatar da shi na tsawon makonni biyu saboda wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter, yana sukar gazawar Gwamnatin Tarayya.
Rubutun dai bai yi wa Gwamnatin Jihar Kanon dadi ba, saboda kusancin Salihun da gwamnatin da kuma mukamin da yake ruke da shi na jami’in gwamnati.
Ya ce, “Na biyu, hukumar ta samu nasarori da daman gaske, a kwana-kwanan nan; idan ba a manta ba lokacin coronavirus da ’yan kasuwa suka kara kudin kayan abinci, hukumar ce ta shige gaba aka sauko da farashin shinkafa – wannan ma nasara ce da ba a taba samun irin ta ba a kasar nan.
“Uwa uba ma ko jami’an gwamnati tsoro suke su yi wani abu na rashin gaskiya saboda hukumar ba za ta bari ba.
“Ta uku ita ce, ban da ita kanta hukumar, yanzu haka an samar da makarantar horar da ma’aikatanta kan dabarun yaki da cin hanci da rashawa sabanin a baya da sai dai a kai ma’aikatan horo Abuja”, inji shi.
Ya ci gaba da cewa, “Ganduje ne jagoran yaki da cin hanci da rashawa saboda maganar gaskiya ake ba ta fatar baki ba.
“Wani abun sha’awa shi ne, ba ya yi wa hukumar katsalandan a ayyukanta, ba ya shiga cikin huruminta.
“Idan ba a manta ba ita dai wannan hukumar ita ce ta bankado maganar bincikar tsohon Sarkin Kano Sanusi II, wanda yanzu haka yana kotu yana ta kokarin yin amfani da kotu ta hana wannan hukumar ta bincike shi.
“Ka ga nan ma wani abu ne babba da babu wanda zai tunanin wannan hukumar za ta iya yin irin wannan aikin”, kamar yadda ya ce, “Rashin tsoma baki da gwamna Ganduje yake yi ga hukumar, abun a yaba wa gwamnati ne”.