Wata babbar kotu da ke zamanta a Kano ta dage ci gaba da sauraron karar zargin sayar da kadarorin gwamnati ga wasu daidaikun mutane a jihar zuwa ranar 29 ga watan Oktoba.
Babbar jam’iyyar adawa ta PDP tana kalubalantar gwamnatin jihar kan yinkurin sayar da otal din Daula mallakin jihar, da wurin ajiye motoci na Shahuci ga wasu manyan ‘yan kasuwa.
A yayin sauraron karar, lauyan masu kara Barista Bashir Yusuf Tudun Wuzirci ya shaida wa kotun cewa gwamnatin jihar ta yi gaban kanta wajen sayar da kadarorin duk kuwa da cewa wata kotu ta bayar da umarnin dakatar da hakan tun da farko.
Ya ce matakin ya saba da tanade-tanaden dokokin da suka fifita mallakar kayayyaki ga gwamnatin fiye ga daidaikun mutane, yana mai cewa ba ta da hurumin sayar da su.
Shi kuwa babban lauyan gwanati kuma Kwamishinan Shari’a na jihar, Barista Musa Abdullahi Lawan ya dage kan cewa gwamnatin na da damar sayar da kadarorin matukar hakan zai amfani jama’a.
Ya kuma musanta zargin cewa gwamnatin ta ki bin umarnin kotu a kan batun, yana mai cewa an tura musu da kwafin hukuncin ne kwanaki biyu da suka wuce, a lokacin kuma an riga an yanke hukuncin sayar da su.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Nura Sagir Umar daga nan ya dage ci gaba da sauron karar har zuwa 29 ga watan Oktoba mai zuwa.