✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje na bincikar kwangilolin da Kwankwaso ya bayar

Gwamnatin Kano na binciken aikin tituna da Gwamnatin Kwankwaso ta bayar a kananan hukumomi 44

Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kwamitin binciken aikin hanyoyi masu tsawon kilomita biya-biyar a kananan hukumomin jihar 44.

Matakin na zuwa ne makonni kadan bayan rahoton Aminiya kan matsayin ayyukan hanyoyin da aka yi watsi da su a jihar.

Ayyukan dai tsohon gwamnan jihar, Rabi’u Musa Kwankwaso ne ya bayar da su, a lokacin gwamna mai ci, Abdullahi Ganduje na mataimakin gwamna kuma Kwamishinan Kananan Hukumomi.

Da ya ke karin haske a kan kafa kwamitin binciken, Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar, Muhammad Garba ya ce gwamnatin jihar ta dauki matakin ne domin yin duba a kan ayyukan, kuma ba za ta yi wata-wata ba wajen soke duk kwangilar da aka gano cuwacuwa a cikinta.

Kwamishinan ya ce kawamitin zai kasance karkashin jagorancin Babban Sakataren Ma’aikatar Ayyuka da kuma wakilai daga Hukumar Tsara Birane ta Jihar (KNUPDA) da Ma’aikatar Kananan Hukumomi a matsayin ‘yan kwamiti.

Malam Muhammad ya ce kwamitin zai gano matsayin aiwatar da kwangilolin da kuma adadin kudaden da aka biya ’yan kwangilar.

A nasa bangaren kuwa, tsohon gwamna Rabi’u Kwankwaso wanda shi ne ya bayar da ayyukan tun da farko ya yi na’am da matakin.

Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnan, wanda kuma yanzu yake zama a matsayin kakakinsa, Kwamaret Aminu Abdulsalam ya ce sun yi maraba da matakin kuma sun dade sun jiran hakan.

“Abin sha’awar shi ne Gwamna Ganduje, a lokacin yana Mataimakin Gwamna shi ne Babban Mai Kula da aikin a fadin jiha”, inji Aminu.

Gwamnatin Kwankwaso ce dai ta bayar da aikin a kananan hukumomi 44 na jihar kafin daga bisani a yi watsi da su bayan saukarta daga mulki.