✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje da Abdullahi Abbas sun shirya tayar da tarzoma a Kano — NNPP

Mun shirya tsaf domin tunkarar duk wasu masu mugun nufi a cewar Kwamishinan ’Yan sandan Kano.

Jam’iyyar NNPP da kakkausar murya ta ce tana zargin akwai wata kitimurmura da shugaban jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya kitsa domin tayar da zaune tsaye a Kano bayan hukuncin Zaben Gwamnan jihar da Kotun Daukaka Kara za ta yanke a yau Juma’a.

Cikin wata sanarwa da ta fitar a Abuja, Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Hon. Abba Kawu Ali, ya ce Ganduje da mukarrabansa sun kitsa tayar da tashin-tashina a Kano.

“Muna samun tabbataccen rahoto cewa Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Abdullahi Umar Ganduje da Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas, sun ba da umarnin a girke ’yan daba a wurare daban cikin birnin Kano wadanda aka dauka haya da manufar tayar da tarzoma idan hukuncin Kotun Daukaka Kara bai yi musu yadda suke so ba.”

Kawu Ali ya tuna da aukuwar irin haka a lokacin zaben 2023 inda aka tara ‘yan daba domin tayar da tarzoma a wurare daban-daban a jihar, ciki har da sakatariyar jam’iyyar NNPP da ke Karamar Hukumar Tudunwada, inda aka kona mambobin jam’iyyar sama da 10 da ransu.

A bisa wannan ne jam’iyyar ta yi kira ga daukacin hukumomin tsaro da su gaggauta dakile wannan mugun nufi da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a jihar.

“Abin takaici ne yadda shugaban jam’iyyar APC na kasa da na jihar duk suke kokarin haifar da rikici a alhali wuri ne da ya kamata su kare ko ta halin kaka,” in ji Abba Kawu.

“Muna kara kira ga daukacin magoya bayan jam’iyyar NNPP na jihar Kano da su kwantar da hankalinsu, su kasance masu bin doka da oda gabanin hukuncin Kotun Daukaka Kara da kuma bayan yanke hukunci, domin muna da kyakkyawan fata cewa za a yi gaskiya da adalci.

A shirye muke — ’Yan sanda

Sai dai rundunar ’yan sandan Kano ta ce an jigbe karin sojoji da ’yan sanda da sauran jami’an tsaro a fadin jihar don wanzar da tsaro gabanin hukuncin da Kotun Daukaka Kara za ta yanke a shari’ar gwamnan jihar.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Mohammed Usaini Gumel ne ya bayyana haka a taron manema labarai da ya gabatar ranar Alhamis da maraice a birnin na Kano.

“Matsayar rundunar ’yan sandan Kano da sojoji da sauran jami’an tsaron jihar ita ce, mun kammala hada gwiwa don daukar dukkan matakan tsaro don tabbatar da zaman lafiya kafin hukuncin Kotun Daukaka Kara da lokacinsa da kuma bayansa.

“Za ku ga cewa mun kara jami’an tsaro na dukkan hukumomin tsaro a muhimman sassa domin tabbatar da ganin ba a fuskanci karya doka da oda ba a dukkan sassan jihar nan,” in ji Kwamishina Gumel.

Ya kara da cewa hukumomin tsaro sun tattauna da wakilan jam’iyyar APC da NNPP “kuma mun amince cewa hanya mafi a’ala ita ce ta tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali kafin hukuncin Kotun Daukaka Kara da lokacin yanke shi da kuma bayansa.”

CP Gumel ya ce, “Mun samu tabbaci daga jam’iyyun biyu cewa za su isar da sako ga magoya bayansu. Muna masu tabbatar muku cewa shugabannin jam’iyyun sun sanya hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya a ofishin kwamishinan ‘yan sanda.”

Yadda aka kwana a ragaya

Tun a ranar 20 ga watan Satumba ne Kotun Sauraren Kararrakin Zabe ta sauke Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan Kano inda ta ayyana jam’iyyar APC a matsayin wadda ta yi nasara a zaben na watan Maris din 2023.

A hukuncin da kotun mai tawagar alkalai uku ta yi a baya, ta ce a kwace shaidar cin zabe da INEC ta bai wa Abba tare da umartar cewa a mika wa Nasiru Yusuf Gawuna ita.

Kotun ta zaizaye kuri’a 165,663 daga kuri’un da Abba Gida-Gida ya samu, inda ta ce ba su da inganci, tana mai cewa ba a manna wa kuri’un 165,663 hatimi ba don haka ba sahihai ba ne.

Sai dai jim kadan bayan hakan, Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya shigar da kara, inda yake kalubalantar hukuncin kotun.

Tun da farko a zaben da aka yi a watan Maris din 2023 Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 1,019,602, sai kuma Nasiru Yusuf Gawuna na APC ya samu 890,705.