✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ganawa da Ubangiji cikin raka’a biyu (5)

Idan ka ce “Assalamu alaikum” kadai ta wadatar.

Idan ka samu kanka a wannan yanayi kamata ya yi zuciyarka ta cika da tsoro, ba tsoro irin na yiwuwar fadawa cikin hadari ko shiga mugun hali ba, a’a tsoro irin na mai kwadayin samun wani abu a hannun wanda ake gudun saba maSa.

A wannan lokacin babu abin da zuciyarka ya kamata ta mallaka face tawassuli zuwa ga Ubangjinka, ta yin addu’ar Ya shirye ka zuwa ga tafarki madaidaci.

Ya taimake ka, Ya datar da kai, Ya budada kirjinka ga bauta maSa Shi kadai, domin ka tsira daga wahalhalun wancan rana mai girma da kaskancin da ke cikinta, ka rabauta da AljannarSa da samun yardarSa!

Wadannan duk su ne ma’anar “Iyyaka na’abudu wa iyyaka nasta’in. Ihdina siradal mustakim. Siradal lazina an amta alaihim. Ghairil maghdubi alihim walad dalin.”

Kana nanata bukatarka ga Allah Ya shiryar da kai zuwa ga tafarki madaidaici, bisa khushu’i da takawa, tare da barranta daga tafarkin Yahudu, wadanda aka yi fushi da su, saboda girman kansu, kuma mai barranta daga tafarkin Nasara, batattu, wadanda suka bace, saboda bidi’o’insu da Allah bai shar’anta musu ba.

Shin akwai lokacin da Musulmi ya fi bukatar wannan shiriya irin yanzu da yake fuskantar manyan hadarurruka da suke iya ruguza shi?

Wannan shi ne sirrin da Allah Ya zaba mana mu rika kaskantar da kai gare Shi da yin wannan addu’a akalla sau goma sha bakwai a kowane wuni.

Bayan Surar Fatiha, sai kuma ka karanto wata surar, misali mu dauki Surar Asri. “Wal’asar. Innal insana lafi khusr.”

Ma’ana Allah Yana cewa: “Ina rantsuwa da zamani. (Cewa): “Lallai mutum yana cikin hasara.”

Babbar magana, yanzu tsayuwar da ka yi a gaban Allah kana maimata cewa mutum hasararre ne! Sai ka auna kanka, kana cikin waccan hasara?

Auna ayyukanka sun dace da umarnin wannan Ubangiji da kake tsaye a gabanSa?

“Illal lazina amanu wa amilus swalihati. Wata wasau bil hakki wata wasau bissabari.”

A nan ga ma’aunin rarrabe wanda ya hasara da wanda ya rabauta. “Face wadanda suka yi imani kuma suka yi aiki na kwarai. Suka yi wa juna wasiyya da yin gaskiya, suka yi wa juna wasiyya da yin hakuri.”

Shin ka yi imani? Ka san ma’anar imanin? Ka dandani zakin imanin?

Shaidar haka ita ce a ga kana aiki na kwarai, a ga kana aikata gaskiya kana umarni da yin gaskiya, a ga kana hakuri kana umarni da yin hakuri ga sauran jama’a.

Idan ba a samu wadannan siffofi a tare da kai ba, aka samu imaninka a fatar baki ya tsaya, ba ka san Allah ba, ba ka san halal da haram da Ya gindaya maka ba, ba ka san komai ba, sai duniya da abin da ke cikinta, to kana cikin hasararru.

Idan aka samu ba ka aikata ayyukan alheri sai cuta da zamba da badala da kwace da kisa da satar dukiyar mutane da bindiga da biro da sauran hanyoyi da cutar da mutane da dabbobi da sauransu kada ka kuskura ka ji a jikinka cewa kana da imani.

Sannan idan ka tsinci kanka ba ka aikata gaskiya ba ka tsare gaskiya ba ka umarta da bayar da shawara ga sauran jama’a su yi gaskiya, ka dauka kai hasararre ne marar rabo!

Wannan shi ne ma’anar wannan sura da ka karanta a takaice, shi ne kake nanatawa a ganawar da kake yi da Ubangijin halittu, Masanin abin da yake boye a zukata, kuma Masanin ha’incin da idanunwa sukeboyewa.

Daga nan sai ka yi ruku’u kana mai maimaita abubuwan da suka gudana a raka’ar farko har zuwa zaman karshe inda za ka yi gaisuwa ga Allah da tashahhudi gare Shi da kuma ManzonSa (SAW) tare da sallama ga (SAW) da sauran bayin Allah nagari.

Hakan na cikin fadinka: “Attahiyyatu lillahi, azzakiyatu lillahi addayabatu salawatu lillahi. Assalamu alaika ayyuhan nabiyyu warahmatullahi wa barakatuhu. Assalamu alaina wa a’ala ibadillahis salihina. Ashhadu an la’ilaha illallahu wa hadahu lasharikalahu, wa asshhadu anna Muhammadan abduhu wa rasulahu.”

A takaice kana mika kyawawan gaisuwa masu tsarki masu dadi ga Allah Wanda kake gabanSa.

Sannan kana sallama da neman rahama da albarka ga Annabi (SAW). Kuma kana sallama ga kanka da sauran bayin Allah salihai.

Sannan ka rufe da kalmar shiga Musulunci Kalmar Shahada kana mai tsarkake Allah cewa Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya, sannan ka karasa da shahada ga Annabi Muhammad (SAW) cewa shi bawanSa ne kuma ManzonSa ne.

Kana iya karawa da yin salati ga Annabi (SAW) da sauran addu’o’in da littattafan Musulunci suka ruwaito, ko ka yi sallama a haka kana mai cewa “Assalamu alaikum wa rahamatullah, sau biyu.

Idan ka ce “Assalamu alaikum” kadai ta wadatar.

Yanzu ka gama Sallah, ka gana da Ubangijinka, sai ka tambayi kanka yaya wannan ganawa ta kasance.

Ganawa ce da ka yi a tsakaninka da Ubangiji kana mai sanin abin da kake fada, ko kuwa ganawa ce da ka yi tsaye kikam kamar turken azara ba ka san abin da ka shaida wa Ubangijinka ba?

Muna fata dan wannan rubutu zai zaburar da mu, mu koma gaban malamai mu dauki ilimi mu san abubuwan da muke fada a yayin Sallah.

Akalla mu yi kokari mu san fassarar ayoyin surorin da muke Sallah da su, ba a ce sai mun san fassarar daukacin Alkur’ani ba, amma wajibi ne mu san na surorin da muke Sallah da su domin mu san abin da kmuke yi a yayin tsayuwarmu a gaban Mahaliccinmu.

Allah Ya datar da mu zuwa ga abin da yake daidai.