✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganawa da Ubangiji cikin raka’a biyu (3)

A ci gaba da warwarar wannan batu na ganawa a tsakanin bawa da Ubangijinsa, a lokacin da yake Sallah, mun tsaya ne a aya ta…

A ci gaba da warwarar wannan batu na ganawa a tsakanin bawa da Ubangijinsa, a lokacin da yake Sallah, mun tsaya ne a aya ta uku, to, yau za mu dora daga aya ta gaba.

Manzon Rahama (SAW), ya ci gaba da bayyani game da wannan muhimmiyar ganawa inda ya ce: “Idan (bawa) ya ce, “Iyyaka na’abudu wa iyyaka nasta’in.” Sai Allah Ya ce, “Wannan tsakaniNa da bawaNa ne, kuma bawaNa yana da abin da ya roka.”

Babbar magana! Idan har aka yi dace Ubangiji Ya fadi haka gare ka a lokacin da kake Sallah, tabbas ka dace, ka rabauta. A ce Ubangiji Ya ce, wannan tsakaninSa ne da kai kuma duk abin da ka roka Ya ba ka, babu sa’adar da ta kai wannan.

Idan ya ce, “Ihdina siradal mustakim. Siradal lazina an amta alaihim. Gairil magdubi alaihim wald dwalin.” Sai Allah Ya ce, “Wannan na bawaNa ne, kuma bawaNa yana da abin da ya roka.”

A nan mai Sallah ya roki Allah Ya shiryar da shi hanya madaidaiciya, hanyar wadanda Ya yi wa ni’ima, su ne Annabawa da salihan bayi, ba wadanda Ya yi fushi da su ba, malamai sun ce su ne Yahudu da masu aiki irin nasu. Kuma ba batattu ba, nan ma malamai sun ce su ne Nasara da masu aiki irin nasu.

Sai Allah Madaukaki Ya ce, “Wannan na bawaNa ne, kuma bawaNa yana da abin da ya roka.” Ma’ana Allah Ya karbi wannan addu’a.

Shin Allah zai karbi addu’a daga wanda bai san me yake roka ba?

Shin Allah zai karbi addu’a daga wanda zuciyarsa take gafalalliya daga sanin cewa yana ganawa ne da Allah?

Shin Allah zai karbi wannan addu’a daga wanda yana Sallah, amma tunaninsa yana can kasuwa ko shago ko ofis ko wurin neman abincinsa?

Ko Allah zai karbi wannan addu’a ce daga wanda ya sakankance cewa wannan Sallah da yake yi, yana ganawa ce da Ubangijin komai da kowa, kuma yana halartowa a zuciyarsa cewa, “Allah ne Mafi girma!” Daga duniya da abin da yake cikinta?

Yanzu mai Sallah ya kammala karanta Surar Fatiha wadda ake kira da Uwar Alkur’ani ko Mabudin Littafi ko Bakwai Masu Daraja da sauran sunayenta.

Surar da ta tattara komai da komai na littattafan da Allah Ya saukar a bayan kasa.

Yanzu bari mu dauki misalin Surar Duha a matsayin wadda mai Sallah zai karanta a raka’ar farko.

“Wadduha. Wallaili iza saja.”

Ma’ana: Allah Madaukaki Yana ce wa masoyinSa (SAW): “Ina rantsuwa da hantsi. Da dare a lokacin da ya rufe (da duhunsa)”

Me ya sa Allah Ya yi rantsuwa da hantsi da kuma dare?  A takaice dukkansu suna da muhimmanci ga rayuwar dan Adam, ma’ana ta kurkusa ita ce, da hantsi dan Adam yake fita neman abinci da sauran bukatun rayuwa sannan da dare yake barci don ya huta.

Mene ne dalilin rantsuwar? “Mawadda’aka rabuka wama kala.”

Ma’ana: “Ubangijinka bai yi maka ban-kwana ba, kuma bai ki ka ba.”

Wato dalilin yin rantsuwar shi ne Allah Madaukaki Yana lallashin masoyinSa tare da ba shi baki kan bakaken maganganun da mushirikan Makka suka rika yi masa ne saboda an samu yankewar saukar wahayi a gare shi a farkon aike.

Bayan lallashin sai kuma aka biya masa da albishir da cewa: “Walal akhiratu khairul laka minal ula.”

Ma’ana: “Kuma lallai ta karshe ce (Lahira) mafi alheri a gare ka daga ta farko (duniya).”

Sannan aka kara da yi masa bushara cewa: “Wala saufa yu’udika rabbuka fatarda.”

Ma’ana: “Kuma lallai ne Ubangijinka zai yi ta ba ka kyauta sai ka yarda.”

Sai kuma Allah Ya sake komawa Yana lallashinsa (SAW) da cewa:

Alam yajdka yatiman fa’awa. Wawajadaka dalan fahada. Wawajdaka a’ilan fa’agna.”

Ma’ana: “Ashe bai same ka maraya ba, sannan Ya yi maka makoma? Kuma Ya same ka ba ka da shari’a, sai Ya shiryar da kai. Kuma Ya same ka matalauci, sai Ya wadata ka?”

Shin dan uwa a lokacin da kake Sallah, kana sane da ma’anar wadannan kalmomi da kake karantawa ko kuwa kawai kana yin Sallar ce ba tare da sanin abin da kake fada ba?

Na tabbata in ba ka sanin ma’anoni abubuwan da kake yi a Sallah, hakika ka rasa dandanon wannan ganawa da kake yi da Ubangijinka, ka rasa alfanun wannan ganawa da kake yi da Allah, ka rasa…ka rasa…ka rasa… ka rasa abubuwa da yawa da suka shafi ganawarka da Ubangiji.

Ka zo ka tsaya a gaban Allah a matsayin kurma, ka yi Sallah a matsayin bebe ka idar da Sallar ka tashi a matsayin makaho!

Ba ka jin kunya a ce ka san komai na yanayin aikinka, ka san komai na harkokin kasuwancinka, ka san komai na yadda kake noma, ka san shige-da-ficen yadda za ka tara dukiya, amma ba ka san abubuwan da kake yi yayin ganawa da Wanda Ya halicce ka Ya ara maka wasu ’yan kwanaki da ba su kai cikin cokali ba, idan aka kwatanta da tekun lokacin da Ya tanada maka a rayuwar Lahira?

Yanzu ba ka jin kunya ka tsaya a gaban Allah kana ta fadin maganganun da ba ka san ma’anarsu ba, balle ka ji a jikinka cewa ga abin da kake fada?

Ka san ka tashi daga Maiduguri zuwa Fatakwal ko daga Kano zuwa Legas ko daga Sakkwato zuwa Kalaba ka je neman kudi, amma ba ka san ka je wurin malamin da ke makwabtaka da gidanku ko yake unguwarku ko yake kauyenku ko yake garinku don ka koyi addini ka san ma’anonin ayoyin da kake karantawa da sauran kalmomin da kake furtawa a lokacin da kake Sallah ba?

Bari mu kammala wannan sura da muka fara karantowa a raka’ar farko.

Sai Allah Ya ci gaba da cewa: “Fa’ammal yatima fala takhar. Wa ammas sa’ila fala tanhar. Wa amma bini’imati rabikka fahaddis.”

Ma’ana: “Saboda haka amma maraya, to, kada ka rinjaye shi (kada ka kwace masa hakkinsa). Kuma amma mai tambaya (mai roko), kada ka yi masa tsawa. Kuma amma ni’imar Ubangijinka, sai ka fada (domin godiya.)”

Wannan lallashi da Allah Ya yi ga fiyayyen halitta in har ka san ma’anar abin da kake karantawa a yayin karatu, za ka ji kai dan gata ne idan ka kwatanta da halin da kake ciki da wanda Annabi (SAW) ya ratso.

Kila kai ka samu iyayenka, kila suna da daula da dukiya.

Shi kuwa bai samu iyayensa ba, a maraya ya taso ya rasa mahaifi kafin ya iso duniya, ya rasa mahaifiya ko shekara bakwai bai kai ba!

Ka sake auna waccan rayuwar da taka.

Ka dauka halin da kake ciki, Allah bai manta da kai ba, bai ki ka ba, kuma in ka yi masa biyayya Lahira za ta fi maka duniya dadi.