Yanzu ka shiga Sallah, kai kadai ne ko kai da liman. Tunda Sallar Asuba ce karatun a bayyane ake yi, don haka a yanzu za ka fara ganawa da Ubangiji.
Ka bayyana a gabanSa kana mai kankan da kai, ka ce, Shi ne Mafi girma daga komai da kowa.
Za ka fara Sallar ce da rokonSa kana mai cewa: “Allahumma ba’id baini wa baina khadayaya kama ba’adta bainal mashriki wal magribi.
Allahumma nakkini minal khadayaya kama yunkas saubu abyadu minad danasi. Allahumma agsilni min khadayaya bi ma’in wa saljin wa bardin.”
Ma’ana: “Ya Ubangiji! Ka nesanta tsakanina da kura-kuraina, kamar yadda Ka nesanta tsakanin mafitar rana da mafadarta.
“Ya Ubangiji! Ka tsabtace ni daga kura-kuraina (zunubai), kamar yadda ake tsabtace farar riga daga dauda.
“Ya Ubangiji! Ka wanke ni daga kura-kuraina da wani ruwa da kankara da sanyi.”
Akwai nau’o’in addu’o’in da ake bude Sallah da su, amma bari mu takaita a kan wannan, mai so yana iya tuntubar malamai don sanin sauran.
Yanzu ka roki Ubangiji Ya wanke ka, Ya tsarkake ka, daga zunubanka da daudar duniya, Ya tsarkake zuciyarka da ruhinka da wani ruwa fari kamar kankara mai sanyi mai sanyaya zuciya da za ta bar tunanin wannan duniya ta koma ga Ubangijinta.
Sai kuma me? Sai ka kori Shaidan a asirce, sannan ka yi Basmalah. Sannan ka fara da cewa:
“Alhamdu lillahi rabbil alamin.”
Shin ka san ma’anar wannan jumla da ka fada? Ko kuwa ka dai fade ta ce yadda ka ji ana fadi? Ko kuwa ka fade ta ce saboda an koya maka yadda ake fadinta a makarantar allo ko Islamiyya, amma ba ka san ma’anarta ba?
Ko kuwa ma wajen karanta ta ba ka fade ta daidai ba, saboda ba ka je makaranta an koya maka ba?
Shin mece ce ma’anar wannan jumla?
Wannan jumla tana nufin dukkan godiya mai dadi mai kyau marar iyaka ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Wato Mahalicci kuma Mamallakin duniya da abin da yake cikinta.
Komai aka gani a bayan kasa naSa ne. Don haka don me za ka zo gabanSa kana tunanin kubucewar wani abin duniya bayan Shi ne Ya mallake shi?
Yadda ka furta cewa Shi ne Ubangijin talikai, me zai hana ka koma gare Shi gaba daya ka yi masa kankan da kai, ka manta da duniya da abin da yake cikinta?
Shin ka san cewa wannan sura da ka fara karantawa aya ta farko daga cikinta ita ce surar da ta kushi duk abin da za ka nema a duniya da Lahira?
Saboda girman wannan sura ce ya sa Allah Ya ce Ya raba Sallah gida biyu a tsakaninSa da bawanSa, kuma Ya yi alkawarin amsar addu’ar da bawan zai yi, kamar yadda Imam Muslim ya ruwaito daga Abu Huraira (RA).
“Manzon Allah (SAW) a cikin Hadisin Kudusi ya ce, “Allah Madaukaki Ya ce, “Na raba Sallah gida biyu a tsakaniNa da bawaNa, kuma bawaNa yana da abin da ya roka.”
Alkawari ne daga Rabbil Izzati, cewa bawa yana da abin da ya roka, Allah zai amsa masa.
Amma kai ka san abin da kake fada a cikin Sallar taka? Shin ka san cewa addu’a kake yi a cikin Sallar, ko dai kana yin ta ce kama ra’aitan nasa?
Manzon Allah (SAW) ya ci gaba da cewa: “Idan (bawa) ya ce “Alhamdu lillahi Rabbil alamin.” Sai Allah Ya ce, “BawaNa ya gode miNi.”
To, yanzu ka gode wa Allah, Shi kuma Ya shaida wa mala’iku mukarrabai cewa ka gode maSa.
Yaya kake ji idan har ka dace Allah Ya ce, ka gode maSa?
Ka auna a ce Gwamna ko Shugaban Kasa ya ambace ka a gaban mukarrabansa cewa wane mutumin kirki ne yana sonsa, shin su ba za su so ka ba? Shin su ba za su girmama ka ba?
Sai Manzon Allah ya kara da cewa: “Idan ya ce “Arrahmanir Rahim.” Sai Allah Ya ce, “BawaNa ya yi yabe Ni.”
Shin ka san ma’anar wannan jumla da ka fadi? Mece ce ma’anar “Arrahmanir rahim?” Tana nufin Allah ne mai gamammiyar rahama, wato mai kyautata ga mai yi maSa da’a da mai saba maSa a nan duniya.
Yana iya ba mai saba masa dukiya da ’ya’ya da mulki, ya hana mai yi masa da’a ko Ya ba su baki dayansu, ko Ya ba su daya ko biyu daga cikin wadannan ni’imomi.
Mai rahama ke nan, Ya yi ruwa a gonar mai yi maSa da’a da fajiri.
Arrahimu kuma mai takaita rahamarSa ga wadanda suka yi imani a ranar Lahira.
A waccan rana ce, Yake nuna soyayyarSa ga masu yi masa da’a, Ya bambanta nagari da mugu.
Ya kebe muminai da jin dadi, Ya bar kafirai da mujirimai da nadama da azaba.
Shin kana halarto haka a lokacin da kake karanta wannan aya a lokacin da kake Sallah? Sai kuma: “Idan ya ce, “Maliki yaumiddin.” Sai Allah Ya ce, “BawaNa ya girmama Ni.”
“Mai nuna mulki a Ranar Sakamako.” Tabbas wannan girmamawa ce ga Allah. Babu wanda zai ce kanzil a wannan rana sai da izinin Allah.
Rana ce da dukiya da ’ya’ya da mata da sanayya da dangantaka ba su da amfani, balle mukami.
Rana ce ta tonon asiri, rana ce ta bakin ciki da damuwa ga wadanda suka yi barna.
Rana ce da mujirimai suke nadamar da ba za ta amfane su ba.
“Ranar da mutum yake gudu daga dan uwansa. Da mahaifiyarsa da mahaifinsa.
“Da matarsa da ’ya’yansa. Kowane mutum a ranar nan akwai wani sha’ani da ya ishe shi.”
Shin a karatun Sallar da kake yi kana kawowa a zuciyarka cewa wannan kalma ta “Maliki yaumid dini,” girmamawa ce ga Ubangiji, ko ka fadi kalmar ce ba tare da sanin ma’anarta ba?
Idan ka sani alhamdulillah. Idan ba ka sani ba, maza ka koma gaban malamai su karantar da kai tun kafin lokaci ya kure maka.
Mu lura tun daga farkon wannan sura bawa yana ganawa ne da Ubangijinsa, yana furta wasu kalmomi da Ubangiji yake mayar masa da amsa.
Koda ba ya jin abin da Ubangijinsa Yake fada, Manzon Rahama (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi mana bayanin ga abin da Allah (Subhanahu Wa Ta’ala) Yake cewa da shi.