✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Game da batun tsawaita wa’adin shugabannin Jam’iyyar APC

Salam Edita, bayan gaisuwa da fatan alkhairi, ina rokon ka bani dama domin tofa albarkacin bakina kan batun tsawaita wa’adin shugabannin jam’iyyar APC ko kuma…

Salam Edita, bayan gaisuwa da fatan alkhairi, ina rokon ka bani dama domin tofa albarkacin bakina kan batun tsawaita wa’adin shugabannin jam’iyyar APC ko kuma saukesu domin zabar wasu sababbi. Babu shakka matukar ana son cigaba da farfadowar dimokuradiyya a kasarmu Najeriya to ya zama wajibi a sauke wadannan shugabannin na Jam’iyyar APC tun da har wa’adin da aka dibar musu ya zo karshe domin shirya sabon zabe tun da ba fin kowa suka yi ba, kuma hakan shi zai bai wa wasu dama su ma su dama da su a matsayinsu na wadanda suka wahala a cikin jam’iyyar, kasancewar kara musu wani wa’adin bayan cikarsa kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanadar yana nuni da cewa akwai handama da babakere a cikin jam’iyyar, kuma hakan ba karamin taka doka da oda ba ne ga gwamnatin Buhari dake bugun kirjin bin doka da oda da

kuma yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.

 

Ashiru Lawal Nagoma Ruwan baure (dan kishin talaka) karamar Hukumar Gusau Jihar Zamfara. 08128828467