Yadda mutane suke kukan cewa ana lalata tarbiyya a tashar Arewa24 ya fara ba ni mamaki.
Dole ne a tambaye ka: Yaya aka yi ka san ana lalata tarbiyya a wannan tashar, kuma me kake so a yi?
Ba mamaki ka san cewa suna lalata tarbiyya ce saboda a gidanka ana kallon tashar. To abin tambaya a nan shi ne, me kake so a yi?
So kake a rufe tashar gaba daya? Kuma in ma rufewar ce, shin wane ne zai rufe?
Don Allah mu rika magana a kan abubuwan da za su yiwu. Ba wai mu rika shiga sharo ba shanu ba.
Ni na taba zantawa da wata tsohuwar ma’aikaciyar tashar Arewa24.
Ta shaida min cewa tashar suna watsa shirye-shiryensu ne daga kasar Jordan ba wai a nan Najeriya ba.
Kuma galibi ko an yi shirye-shiryen a nan Najeriya, to, yakan dauki kamar wata uku zuwa shida kafin a aika kasar Jordan, don a watsa a kan tauraron dan Adam domin mutanen duniya su sha kallo!
Ka ga ke nan, akalla wannan ya nuna cewa tashar tana da tanadi na isassun shirye-shiryenta na akalla wata uku zuwa shida.
Wannan shi ne Bature ke cewa “reservoir” wato rumbu. Ko yau suka tsaya aiki cik, to za su iya ci gaba da watsa muku shirye-shirye har na wata uku zuwa shida.
To yanzu idan kana kuka da tashar nan, me kake so a yi?
Na farko dai ba ma daga nan Najeriya suke watso ‘badalar’ ba, balle ka ce gwamnati ta saka musu takunkumi.
Kasashen Larabawa kuma a yau, ai ba sai an ba ka labari ba, sun fi kowa son sharholiya irin wanda ake zargin Arewa24 da watsawa.
Don haka, maganar ma cewa kasar Jordan ta dakatar da su ba ta taso ba.
Don ba ka ma isa ba, musamman idan da gaske kasar Amurka ce take kaukar nauyin tashar.
Kai bari in fada maka gaskiya:
1. Tarbiyyar iyalinka nauyinka ne; Babu wanda zai zo ya taya ka wannan aiki na wajibi.
Yadda ka ga babu wanda yake taya ka yin Sallah da azumi, to babu wanda zai zo ya taya ka yin tarbiyyar iyalinka.
2. In ka fahimci wannan, to sai ka san cewa tunda dai kai ne da kanka ka sayo StarTimes da GoTV da DSTV ka kafa, to dole ka yi hakuri ka karbi duk abin da ya biyo baya.
Ai duk wanda ya sayi rariya, ya kamata a ce ya san za ta zub da ruwa ko?
Ko dai ka san yadda za ka yi wajen kula da yadda ake kallon nan, ko kuma dole ka yi hakuri da abin da za ka gani.
3. Idan kana ganin ba za ka iya takura wa iyalinka ba a kan kallon talabijin, to ka sani, su masu tasha ba fa za su fasa kasuwancinsu da yada manufarsu ba. Yadda ba ka so ka takura kanka, su ma ba su son takura!
4. Kuma in ban da yaudarar kai, fisabilillahi kai a matsayinka na mai gida, mai cikakken iko a kan gidanka, ka kasa hana kallon tashar, amma kuma kake tsammanin gwamnatin Najeriya ko ta Jordan ta hana wadannan mutanen yada manufarsu?
Kai ma ai ‘Shugaban Kasar Gidanka’ ne; Yaya aka yi ka kasa korar tashar daga gidanka?
Gazawa ko? To ita ma gwamnatin ta gaza. Don haka ka yi hakuri ka karba a haka.
Wannan tasha tana da mabiya da yawa. Ana kallon ta sosai, tun daga gidajen masu kudi har na talakawa; gidajen jahilai da gidajen malamai; Mata da maza, yara da manya, duk fa kallo ake.
Wallahi ana kallo! Kuma yaya za a yi kai ka kasa hanawa a gidanka, amma kake tsammanin kawai za a wayi gari an toshe tashar?
Haba Alhaji! Ba ka ji Baba Buharin ya ce “Change Begins With Me” ba, wato gyara ya fara daga ni kaina?
Ai ka gyara gida kawai. Wancan ya gyara. Idan duk aka gyara, tashar za ta mutu da kanta.
A Facebook kwanaki muka sha fama da wani hashtag wai #Labarina_Series.
Mutane suka cika mana newsfeed da wannan hashtag, daga mata har maza; yara da manya; Yadda dai masoya kwallo ke damunmu lokacin wata gasar kwallo. Wannan ke nuna maka ana kallon tashar sosai.
Ni ina ganin da kun yi hakuri kun kalli tasharku kawai. Duk wannan bayanan cewa a rufe tashar, ko a fara tacewa, ko cewa shirin Yahudawa ne, duk ba zai muku wani amfani ba. Zancen kawai kuke.
Kada mai karatu ya yi tambaya cewa yaya aka yi Ibrahim ya san tashar.
Gaskiya a shekarar 2018 na kalli wasu bangarori na shirin “Dadin Kowa” a tashar.
To da yake ba na zama sosai, kuma na gaji da yin “sadaka” ga GoTV wajen biyan kudin kallon shirye-shiryensu, sai na daina biya.
A shekarar 2019 na kyautar da tawa. Don haka ni yanzu ba ni da matsala da Arewa24.
Ni Facebook ne sharrin Yahudun da ya kama ni, ba talabijin ba.
Ibrahiym A. El-Caleel ne ya rubuto wannan maqalar.
Za a iya samunsa ta imel: caleelcv@yahoo.co.uk