✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gambo Muhammed ya koma Kano Pillars

Fitaccen dan wasan kungiyuar kwallon kafa ta Kano Pillars Gambo Muhammed ya koma kulob dinsa bayan da aka kasa cimma matsya a tsakanin kulob din…

Fitaccen dan wasan kungiyuar kwallon kafa ta Kano Pillars Gambo Muhammed ya koma kulob dinsa bayan da aka kasa cimma matsya a tsakanin kulob din Pillars da  na Filato United wadanda suka nuna sha’awar daukar hayar dan wasan na wani lokaci.

Rahotanni sun bayyana cewa an kasa samun daidaito ne tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Kano Plllars da kuma ta Filato United a kan kudi Naira miliyan 15 da Pillars din ta nemi Filato United ta biya a matsayin kudin daukar dan wasa Gambo Mohammed lamarin da kungiyar ta Filato ta nuna kudin ya yi mata tsada kamar yadda aka rawaito cewa Janar Manaja na Kulob din Filato United Mista Pius Henwan ya bayyana.

Mista Henwan ya kara da cewa “a gaskiya mun so daukarsa amma daga tattaunawar da muka yi da shugabannin kulob din Kano Pillars a kan kudin da za mu biya, inda muka ga Naira miliyan 15 da suka nema sun tsorata mu, hakan ya jawo muka soke batun daukarsa don buga mana wassa a kakar wasanni ta shekarar 2017 zuwa 2018.”

A cewarsa babu yadda ba su yi da Kano Pillars ta rage farashin  daukar dan wasan ba amma ta ki inda ta dage akan farashin da ta sanya tun da farko.

Da yake zantawa da manema labarai Shugaban kungiyar  Kano Pillars Alhaji Tukur Babangida ya bayyana cewa tun da dai dan wasansu ne wanann ba sabon abu ba ne idan wani dan wasa ya bar kulob dinsa sannan daga baya ya dawo. “Da ma dan wasanmu ne, don haka tuni ya dawo gida ya shiga cikin ‘yan uwansa don samun karin horo. Na tabbata zai yi abin da ya yi a baya wajen samun nasara a wasanni” Inji shi.