Tsohon dan wasan gaba na Najeriya da Kano Pillars Gambo Muhammad ya zama mataimakin mai horarwa a tawagar Sai Masu Gida.
Gambo Muhammad ya koma Pillars ne bayan kammala karatun aikin horarwa a kwalejin harkokin wasanni ta kasa da ke birnin tarayya Abuja.
- Damiba ya karbi rantsuwar kama mulki a Burkina Faso
- Mun dauki matakan kawo karshen karancin mai —NNPC
Mai magana da yawun kungiyar Rilwanu Idris Malikawa Garu ne ya sanar da hakan, gabanin wasan da Pillars za ta karbi bakoncin Plateau United a gasar NFPL.
Bayanai sun ce Rilwanu Idris Malikawa Garu da shugaban kungiyar Alhaji Surajo Shuaibu Jambul ne suka yi uwa suka yi makarbiya wajen ganin Gambo ya koma wannan kungiya a matsayin mai horarwa, la’akari da irin gudunmawar da ya ba ta a lokacin yana dan wasa.
Gambo Muhammad dai ya shafe shekaru da dama a matsayin dan wasa a Kano Pillars FC, inda ya jagoranci tawagar lashe gasar firimiya har hudu, kafin daga bisani ya koma Katsina Utd wanda ya shafe kakar wasanni biyu a can.
Jim kadan bayan amincewa da aiki a tawagar ta Kano Pillars Gambo Muhammad ya gode wa shugaban kungiyar Surajo Shu’aibu Jambul, wanda ya yi alkawarin zai ba da gudunmawa domin ci gaban kungiyar.