A ci gaba da gasar cin kofin nahiyar Afirka da ke gudana a kasar Kamaru a zagaye na biyu, kasar Gambiya ta fitar da kasar Guinea bayan ta yi nasara a kanta.
A yammacin ranar Litinin ne tawagar kasashen biyu suka kece raini, sai dai Gambiya ce ta yi nasara a kan Guinea da ci daya mai ban haushi.
- A shirye nake in sa hannu a hukuncin kisa kan makashin Hanifa – Ganduje
- AFCON2021: Dalilai 3 da suka sa aka yi waje da Najeriya
Dan wasan gaban tawagar ta Gambiya, Musa Barrow, ne ya jefa kwallo a minti na 71, yayin wasan da aka fafata a filin wasa na Kouekong, da ke kasar ta Kamaru.
Har aka tafi hutun rabin lokaci dai, babu daya daga cikin kasashen da ta sami damar jefa kwallo a ragar abokiyar hammayarta.
Yanzu haka dai Gambiya ta samu tikitin zuwa zagaye na uku na gasar ke nan.