✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gambiya: Me zai biyo bayan zaben shugaban kasa?

A yau al'ummar Gambiya ke fita don zaben shugaban kasa

Ranar Asabar ne al’ummar kasar Gambiya ke zaben shugaban kasa.  

Shugaban kasa mai ci, Adama Barrow yana neman tazarce, kuma a wannan karon ya zo da wani babban al’amari inda ya kulla kawance da jam’iyyar tsohon shugaban kasar Yahya Jameh.

A hannun Jameh ne dai Baron ya karbi mulki bayan kai ruwa rana a 2017.

Bayan zaben ne dai aka kori Jameh daga kasar kan wasu laifuka da ake tuhumar shi da aikatawa na kama karya, fyade da keta hakkin dan Adam.

Wannan ya sa ake ta tunanin yadda makomar kasar za ta kasance bayan kammala zaben na 2021.

A kan haka ne Aminiya ta tattauna da Dokta Tukur Abdulkadir, mai sharhi a kan al’amuran siyasar duniya kuma malami a Sashen Kimiyyar Siyasa na Jami’ar Jihar Kaduna (KASU).

Aminiya: Me za ka ce dangane da yadda Shugaba Adama Barrow da tsohon  shugaban kasar, Yahya Jameh suka hada kai gabannin zaben da za a yi kuma me hadewar tasu take nunawa?

Dokta Tukur Abdulkadir: A ganina ba wai sun hade guri daya ne ba — a’a jam’iyyun da suke ne suka hade da juna, kasancewa shi Adama Barrow ya samu matsala da jam’iyyarsa tun da ka san da ma ya yi alkawarin shekara uku zai yi.

Sannan kuma kamar rikon kwarya ne zai yi, sai ya kasance ya canja alkawarin da ya dauka wanda ya sa aka samu baraka a jam’iyyarsa, sai ya kirkiro sabuwar jam’iyyar kuma aka samu alaka tsakaninsa da shi tsohon shugaban kuma har yanzu ba za a ce suna tare ba, saboda daya dan takarar yake goyon baya.

Wannan din ya sa an samu baraka a jam’iyyar da ma gurin wasu ’yan kasar saboda an samu wadanda ba su ba shi goyon baya ba, kawai dai za a iya cewa alakar tasu tana kasa tana dabo.

Ka yi bayanin cewa alakar tasu tana kasa  tana dabo, yaya za a yi hasashen makomar alakar idan aka ci zabe ko aka samu akasin haka?

Ka san cewa gwamnatin Adama Barrow ta samu nakasu inda wasu ke ganin gwamnatin ta gaza cika alkawuran da ta dauka na magance matsalolin keta haddi da ake zargin gwamnatin baya ta yi da ma sauran abubuwa, kuma har yanzu Jameh yana da farin jini a wasu wurare musamman a karkara, kuma da ma siyasar Afirka gaba daya ta ginu ne a kan kabilancin addini ko yare, za ka ga duk nakasun shugaba in dai ya fito daga yankinka, kawai za ka so shi ba tare da [la’akari da] cancanta ba.

Shin za a iya cewa shugaban na yanzu ya zabi komawa ita wannan jam’iyyar ce domin ya yi amfani da wannan damar wajen samun nasara a zaben?

Ka san cewa ba shi kadai ke hakan ba, kusan duka ’yan takara na yi, kawai dai ya danganta da tasirin da wannan kira zai yi, kasancewar ’yan kasar musamman matasa har yanzu na fuskantar matsaloli musamman rashin aikin yi tun da dama sun fi dogara ne da harkar yawon bude ido wajen samun kudin shiga kuma sai ga shi tun daga bullar COVID-19 wannan harka ta samu nakasu.

Wannan ya kara yawan marasa aikin yi.

Shin akwai wani sauyi da hadewar za ta kawo a siyasar kasar?

Zai yi wahala gaskiya, sai dai in suka ci zabe kila za a iya samun canji a siyasar kasar, kila a iya janye zarge-zargen da ake yi wa shi Yahya Jammeh.

Sannan kila za a iya ba shi dama ya dawo rayuwa a kasar.

Kila kuma a samu a tabarbarewar al’amura a kasar saboda da ma zaman lafiyar bai wadata ba a kasar tun a waccan gwamnatin da ta shude.

Wane tasiri wannan zaben zai yi ga makomar siyasar kasar?

In dai an yi lafiya zai iya ba da damar samun shugabanci a kasar na gari; kila yadda jama’a za su ji dadin yadda aka gudanar da zaben lafiya kuma sahihi zai karfafa hatta sauran yankuna na Afirka da suke fuskantar matsalalar zabe kamar Afirka ta Kudu da Namibiya da sauransu.