✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Galibin kananan hukumomin da suka fi masu COVID-19 a Legas suke

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce 11 daga cikin kananan hukumomi 20 da suka fi yawan wadanda suka kamu da…

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce 11 daga cikin kananan hukumomi 20 da suka fi yawan wadanda suka kamu da COVID-19 a Najeriya a jihar Legas suke.

Hukumar ta bayyana hakan ne a wani rahoto da ta fitar wanda ke nuna kananan hukumomin da suka yawana mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus.

Rahoton ya nuna cewa karamar hukumar Mainland ta jihar ta Legas ce kan gaba da mutane 1,274 da aka tabbatar sun kamu da cutar.

Sauran kananan hukumomin da ke da yawan masu cutar a jihar sun hada da Mushin mai mutane 458, Eti-Osa mai 403, Alimosho mai 239, sai Kosofe 175, Ikeja 168, Oshodi/Isolo 132, Apapa 131, Amuwo Odofin 129, sai Lagos Island mai 111 yayin da Surulere ke da mutum 110.

A Yankin Babban Birnin Tarayya kuwa, karamar hukumar Birnin Abuja da Kewaye ce kan gaba da mutum 536 yayin da karamar hukumar Tarauni a jihar Kano ke biye mata baya da mutune 248.

Hakazalika, karamar hukumar Katsina da ke jihar Katsina na da mutum 242, a Maidugurin jihar Borno akwai mutum 167, Dutse a jihar Jigawa 170, Nasarawa a jihar Kano 152, Oredo a jihar Edo 126, sai karamar hukumar Bauchi a jihar Bauchi mai 114 yayin da Ado Odo/Ota a jihar Ogun  ke da mutum 107.

Rahoton na NCDC ya kuma ce zuwa 30 ga watan Mayun da ya gabata, kimanin mutum 62,583 ne aka yi wa gwaji a fadin Najeriya, a ciki kuma 10,023 aka tabbatar suna dauke da cutar.

Hukumar dai ta wallafa a shafinta na Twitter cewa zuwa yanzu, mutum 3,122 daga cikin 10,578 ne suka warke kuma tuni aka sallame su, wasu 299 kuma su ka kwanta dama.