Galadiman Masarautar Jama’a da ke Karamar Hukumar Jama’a ta Jihar Kaduna, Alhaji Bala Mohammed, ya rasu.
Ya rasu ne ranar Asabar da daddare kuma tuni aka yi jana’izarsa da safiyar Lahadi a garin Kafanchan.
- Likitan bogi da ya auri mata 27 ta hanyar yaudara ya shiga hannu
- An ba hammata iska tsakanin mabiya addinin Hindu da Musulmai a Indiya
Galadiman Jama’a wanda shi ne Shugaban masu zaben sarki a masarautar ya rasu yana da shekara 73 a duniya.
A cikin takardar sanarwa da Masarautar ta Jama’a ta fitar da ke dauke da sa hannun Sakatarenta, Alhaji Yakubu Isa (Dokajen Jama’a), ta bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga masarautar baki daya.
Sanarwar ta bayyana marigayin a matsayin jajirtacce abin koyi, inda ta mika ta’aziyya ga iyalansa da sauran al’ummar masarautar gaba daya.
An dai haifi marigayin a shekarar 1949 a garin Kafanchan da ke Jihar Kaduna.
Ya fara karatun Elimentare a shekarar 1958 ya kuma kammala a shekarar 1965.
A tsakanin shekarar 1966 zuwa 1968, ya yi aiki da kamfanin masaka na Kaduna.
A shekarar 1980 ne ya fara aiki a kotu a matsayin alkali a garin Kwoi da ke Karamar Hukumar Jaba a yanzu, sannan daga baya ya koma Kotun Daukaka Kara ta Shari’ar Musulunci da ke garin Kafanchan a matsayin babban alkali.
Ya gaji mahaifinsa inda aka nada shi a matsayin Galadiman Jama’a a ranar uku ga watan Fabrairun shekarar 1997.
Marigayi Galadima ya rasu ya bar matan aure biyu da ’ya’ya hudu, ciki har da matar Sarkin Jama’a da matar Dan Madamin Jama’a da matar Matawallen Jama’a sai namiji guda daya.
An yi jana’izarsa ranar Lahadi kamar yadda addinin musulunci ya tanada a garin Kafanchan.