Cibiyar Shari’a ta kasa ta zabi tsohon alkalin kotun koli, Sulaiman Galadima a matsayin shugaban kwamitin sanya ido na shari’ar cin hanci da rashawa.
Sulaiman Galadima ya maye gurbin mai shari’a Ayo Salami mai ritaya wanda ya nemi ya ajiye mukaminsa na shugaban kwamitin.
Wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Cibiyar, Soji Oye ya sanyawa hannu ya ce za a kaddamar da kwamitin ranar Laraba.
Kuma Babban Mai Shari’a Na Kasa, Walter Onnoghen shi zai kaddamar da kwamitin a dakin taron na cibiyar da misalin karfe 2 na rana.