Gagarumar gararumar Girgoriya
Gargarar kwanakin shekara
Wadanda suka shude aka tara
Sabuwar kirga aka fara
Yawan kwanaki aka bibiya
Tuni aka bude babin Hijiriyya
Kwanaki sun yi zirya
Makonni sun yi jerangiyya
Watanni ake ta kidaya
Masu kirge na tattara tariya
Mabudi
Abin warware kulli
A samar da kafar bulli
Ballin maballi
Ai babu rudi
Ga goro
Goriya kwararo-kwararo
Sange sanhon sunkutar sauro
Samarin kusu a soro
Mahukunta na ta taro
Kolo zai ga budi
Titibiri an sammasa sudi
Ga sauran madi
A dan tauna ridi
Malam na ta hankoron badi
Tsohuwa sai ta ji dadi
An samu zaren kadi
Dan mazari na tsallen kwadi
Kada na ta tumbudi
Goriyar goro da gardi
Mai Magana da kaudi
Tambadar yamadidi
Gayyar na gayyaron sodi
Daga bara zuwa badi
Aka fasko masu rawar kidi
Kwankwadar modar modi
Wasu sun salwantar da kudi
Ayyuka na hanzarin dodon kodi
Na-mujiya baibye da burbudi
Lamura na sararaf sididi
Magarkama
Makwararar makama
Magangarar masu himma
Gajiya na sa hamma
Gayu na ta hauma-hauma
Mabubbuga
Mahanga
Mai kwarar damar sanga
Kwaranyar kaya ba daga
Ko taka kwaranga
A dai leka ta taga
’Yan kwadago ai jinga
Karin lada ake ta kirga
Labarai aka kaga
Nika da sara ke da dudduga
Masunta su dumfari Baga
Argungawa sun ja zuga
Ja-hadewa na Jijjiga
Kayan miya uwargida ta jajjaga
Masu fafutika an ja tunga
Haramar hijiriya
Gangamin Girgoriya
Lissafin kwanakin duniya
Damarar mutan Haurobiya
Tsillin matsaloli soke a kibiya
Gwamnati tai kasafi
Mun wasa balati tai kaifi
Za mu yanki abin hasafi
Ka da dai mui laifi
Mu cika ciki mui tufafi
’Yan dugwi-dugwi ga tallafi
Masu agaji ai wakafi
Ai girka miyar farfesun kifi
A kawar da cuta masu dafi
Gidaddaji ai musu rufi
Masu zuwa rafi
Ai musu burtsatse mai rufi
Sha da shayarwa tai kafi
Ba sauran zuwa kududdufi
Mabubbugar ruwa za mui dafifi
Ci da ciyarwa
Sha da shayarwa
Biyayyar bibiya da baiwa
Tsarin ga da ban shawa
Kowa ya diba ba kokowa
Al’umma
A hada karfi da hukuma
Mahukunta ban da hadama
Kowa yai kama-kama
Don a samu makama
Baban-burin-huriyya
Ka kara kaimin kariya
Da aiki a Haurobiuya
Tunkarar miyagun turjiya
Ka da dai a gajiya
Saurayin-kirinki
Ban da kwaramniyar bariki
Ka daina bugun taiki
Ka wancakalar da jaki
Lallai ka lizimci aikin kirki
Dogarin rafkiya
Kai karo da kofaton kwafdiya
Ka yasar da waskiya
Da kwarakar karafkiya
Ko kutungwilar tsiya
Samarin-kusu
Ku yi watsi da kurmusu
Wai ku kosassu
Talakawanku busassu
Tekun zari-ruga ku as sarakan su
A daina duma wasoso
A hana talaka wankan sabulun soso
Miyagu na ta rawar koroso
Mara galihu yai kafar kaujen faso
Ko dai haka ake so
Mai sana’ar na-duke
Yabanya in ta sarke
Ka daina sake-sake
Ban da noke-noke
Wajen aiki sai a kuke
Damina rani da kaka
Ai ta turka-turka
A gayauna da garka
Kiwon bisashe ba shakka
Sa’a ce aka taika
Jaddawalin zabuka
Ana ta zabarin zababbaka
Fatanmu kar ai aika-aika
Masu zabi-sonka
Kowa ya dukufa da fafutika
Mu zabo nagargaru
Na- mujiyarmu na gani kuru-kuru
Ka da a ce mun kuru
An fasko kaji da zakaru
Shugabanni su zam zakakuru
Ai karatun babbaku da farfaru
Mu fasko masu shigar sunkuru
Da ke mana ’yan dabarbaru
Manufarsu tauna gurguru
Talakawa tsiyaku nai musu guru
Jama’a
Miyagun ayyuka mu ce a’a
Mu yasar da wargin ba’a
Alwallarmu ba lam’a
Tafarkin rayuwa ya zam sa’a
Mu dai mui da’a
Da kyautata dabi’a
Fuskokinmu su zam fara’a
Mui fafutikar sana’a
Da warware sasarin San’a’a