✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gado ya sa ni shiga siyasa – Halima Shata

Hajiya Halima Mamman Shata, daya daga cikin ’ya’yan shahararren mawakin Hausar nan, Alhaji Mamman Shata Katsina ta bayyana cewa ta shiga siyasa ce domin ta…

Hajiya Halima Mamman Shata, daya daga cikin ’ya’yan shahararren mawakin Hausar nan, Alhaji Mamman Shata Katsina ta bayyana cewa ta shiga siyasa ce domin ta gaji mahifinta inda take shirin tsayawa takarar Majalisar Dokokin Jihar Katsina daga mazabar Funtuiwa a zaben 2019. 

Lokacin da ta zanta da wakilinmu kan shigarta siyasa da kuma tsayawa takara duk da kasancewarta mace, ta ce, “Baya ga gadon siyasa da na yi daga wajen mahaifina Dokta Mamman Shata, kuma na shiga siyasa ce don in ba da gudunmawata ga ci gaban karamar Hukumar Funtua da kawo kudirorin da za su kawo sauyi da ci gaban mata gami da inganta rayuwarsu a jihar Katsina da kasa baki daya.”

Halima Shata ta kara da cewa “Mata suna da rawar da za su taka, a fagen siyasa, amma mun yi barci an bar mu baya musamman a Arewacin Najeriya. kalilan ne ke fitowa takara, saboda wasu dalilai. Kuma mu mata mu ne muka fi fitowa a ranar zabe, kuma kullum mu ne ake bari a baya. To idan Allah Ya ba ni nasara zan tabbatar da an yi dokokin da za su inganta rayuwar matan Jihar Katsina da kuma karfafa rayuwarsu.” 

Ta kara da cewa, tana ci gaba da samun kwarin gwiwa a harkar siyasar daga jama’a saboda kowa ya san mahaifinta dan siyasa ne, kuma ta tashi ta iske mahaifinta yana harkokin siyasa har ya taba zama shugaban jam’iyya kuma ya nemi tsayawa takarar Shugaban kasa nan. “Ina alfahari in gaje shi a bangaren siyasa, kuma zan ci gaba da mayar da hankali domin ganin na kai ga nasara,” inji ta. 

Ta yaba wa Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari bisa irin goyon baya da kwarin gwiwa da yake nuna wa mata a kan su fito a dama da su a harkokin siyasa a jihar, inda ta bayar da misali da bai wa mata manyan mukamai a gwamnatinsa.