✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gaba da gaban da wakilinmu ya yi da Bello Turji

Tafiya ce mai cike da kasada, da sai da rai, ko kuma abin da wadansu za su ce ganganci.

Wakilin jaridar Aminiya da gidan talabijin na Trust TV, Abdul’aziz Abdul’aziz ya samu ganawa gaba da gaba da dan bindigar nan da ya yi kaurin suna, Bello Turji, a wani bangare na wani bincike mai zurfi a kan tashe-tashen hankalin da ke faruwa a wasu sassan Arewacin Najeriya.

Tafiya ce mai cike da kasada, da sai da rai, ko kuma abin da wadansu za su ce ganganci, musamman ganin ta faru ne a daidai lokacin da sojoji da sauran jami’an tsaro suke ikirarin yin luguden wuta a sassan da ’yan bindigar suke zaune a dazukan jihohin Sakkwato da Zamfara.

A cikin wannan yanayi ne wakilinmu ya yi shigar burtu ya kai ziyarar gani-da-ido dajin da ke tsakanin Karamar Hukumar Shinkafi a Jihar Zamfara da wani sashi na Karamar Hukumar Isa da ke Jihar Sakkwato.

Niyyar tafiyar ita ce ganawa da rikakken dan fashin dajin nan, Bello Turji. Bello Turji ya yi kaurin suna musamman a baya-bayan nan sakamakon tashin hankali da hare-haren ’yan bindiga a kan iyakokin Zamfara da Sakkwato wanda Turji da mutanensa ke jagoranta suka haifar.

A cewarsu sun yi haka ne don mai da martini kan kashe ’yan uwansu makiyaya a wasu daga cikin kauyukan da ke wannan shiyya.

A tsawon kusan shekara uku zuwa hudu, Bello Turji, wanda haifaffen kauyen Fakai ne da ke gabashin Shinkafi, ya yi ta fadada dakarunsa na matasan ’yan bindiga wadanda da su ne yake amfani domin satar shanu da sauran hare-haren ta’addanci a kan mazauna garuruwan da ke kewaye da mazauninsa.

Sai dai a karshen shekarar 2021, Turji ya nuna niyyarsa ta neman zaman lafiya tare da ajiye makamansa.

Wannan dalili ne ya sa wakilinmu ya yi tattaki don ganawa da dan bindigar domin gane wa idonsa da kuma tattaunawa da Bello Turji kan wannan aika-aika da shi da mutanensa suke yi.

Wakilinmu ya yi tattaunawa mai tsawo da Turji kuma ya gane wa idanunsa sauran mayakan da ke addabar wannan shiyya, irin su Yalo Danbokolo da Ummaru Nagona da Yalon Emiya da Auta Bubaje da Kachalla Mingel da Malam Ila Manawa da Baleri Fakai.

Domin kara fahimtar tushen matsalar da ke faruwa ta kashekashen mutane a wannan yanki, wakilin namu ya kuma ziyarci wasu garuruwa a jihohin Katsina da Zakkwato da Zamfara don tattaunawa da wadanda abin ya shafa.

Domin samun cikakken bayani kan wannan bincike da kuma hirarmu da Bello Turji, a tara a mako mai zuwa a wannan jarida ta Aminiya.