Hukumar Kula da Gidajen Gyara Hali a Najeriya (NCS), ta fitar da sunaye da hotunan wadanda ake zargin ’yan ta’addan kungiyar Boko Haram ne da suka tsere daga gidan yarin Kuje da ke Abuja.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a, hukumar ta ayyana mayakan kungiyar 69 a matsayin wadanda take nemansu ruwa a jallo.
Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar 5 ga watan Yuli, wasu ’yan bindiga suka far wa gidan yarin na Kuje da ke babban birnin kasar, inda suka kubutar da mutane da dama, ciki har da fursunonin da ake zargin mayakan Boko Haram ne, wadanda ake tsare da su.
“Wadannan su ne fuskoki da sunayen fursunoni da ake musu shari’a kan alaka da kungiyar ta’addanci/Boko Haram, wadanda suka tsere daga gidan yarin Kuje a lokacin da aka kai hari a ranar 5 ga watan Yuli,” a cewar Sanarwar Hukumar Kula da Gidajen Gyara Halin.
“Idan ka ga daya daga cikin wadannan mutane, ko kuma kana da bayanai masu amfani da za su kai ga sake kama su, sai ka kira daya daga cikin wadannan lambobin waya kamar haka: 07000099999, 09060004598 ko 08075050006.
“Ko kuma a gaggauta mika rahoton ga duk wata hukuma mai tilasta kiyaye doka da oda da ke kusa da ku. Muna baku garantin boye bayananku.”
Sunayen wadanda ake nema ruwa a jallo
Mutanen sun hada da Abdulkareem Musa, Abdusalami Adamu, Abubakar Abdulrahman Habibu, Abubakar Mohammed Sadiq, Abubakar Mohammed, Abubakar Yusuf, Adam Lawal Muhammad, Akibu Musa Danjuma, Amodu Omale Salihu, Bello Haruna, Bilyaminu Usman, Bukar Ali, Ibrahim Mohammed, Ikya Abur, Ismail Idris Abdullahi, Modu Aji, Mohammed Sani, da Musa Abubakar.
Sauran sun hada da Mustapha Umar, Mustapha Umar, Shehu Abdullahi, Suleiman Idi, Suleiman Zacharia, Sunday Micheal, Yakubu Abdullahi, Yasir Ibrahim Salihu, Yunusa Mukaiya, Abdulmannan Obadiki, Abubakar Mohammed Musa, Abubakar Umar, Adamu Mohammed, Ahmadu Hagola, and Asama Haruna Kanti, Baluye Modu, Bassey Victor Kingsley, Diko Iko, Fannami Alhaji Bukar, Faruku Waziri, Hassan Hassan, Ibrahim Musa, Idris Ojo, da Ishaq Farouk.
Kazalika akwai, Mohammed Goni Kyari, Mohammed Guja, Mohammed Saleh Buba, Mohammed Umar, Mukhtar Ussaini Khalidu, Musa Adamu, Musa Umar, Onyemire Asagba, Rabiu Shaibu, Sahabi Ismail, Sani Mohammed, Umar Ahmadu Ladan, Usman Balarebe, Yahaya Adamu Abubakar, Yusuf Yakubu, Abdulazeez Obadaki, Auwal Abubakar, Mansur Mohammed Usman, Mohammed Abubakar, Mohammed Jamiu Eneji Sani, Muazu Abubakar, Muhammed Sani Adamu, Muktar Umar, Nambil Zakari Gambo, Sadiq Garba Abubakar, Yazid Muhammed Usman, Yusuf Ali Yusuf.
Fuskokin wadanda ake nema ruwa a jallo