Fulani ’yan gudun hirija suna cikin tsaka mai wuya inda suke fuskantar tsangwama a Kananan Hukumomin Munya da Shiroro na Jihar Neja.
Daruruwan Fulani ’yan gudu hijira, yawancinsu mata da kananan yara na zaune cikin zullumi saboda tsoron wasu kabilu da ke kai farmaki a kauyukan Fulani za su kai musu hari.
- Rashin tsaro: Babu wanda ya tsira a Najeriya —Dahiru Bauchi
- Rashin fada wa gwamnati gaskiya ne ya jefa Najeriya cikin rikici — Osinbajo
- Dole a yi asusun musamman don yakar ta’addanci
- ’Yan bindiga sun kashe miji da matarsa a Benuwai
Hakan na zuwa ne bayan hare-haren ’yan bindiga sun tilasta wa akalla mutum 5,000 daga kauyuka daban-baban neman mafaka a Fadar Sarkin Minna, inda daga baya aka yi musu matsuguni a makarantar firamaren IBB da ke garin Minna.
Sai dai tsoron wasu kabilu za su kai musu hari, ya sa Fulani ’yan gudun hijira neman mafaka a wasu wuraren.
Aminiya ta gano wasu ’yan gudun hijirar na barin sansanin; wasunsu na komawa wurin ’yan uwansu a wasu kauyuka, zuwa lokacin da al’amura za su daidaita.
Hukumar Bayar da Agaji ta Jihar Neja (NSEMA) ta ce tana zagayawa a garin Minna domin daukar bayanan ’yan gudun hijirar da ke zaune a gidajen al’umma.
Darakta-Janar na Hukumar, Ibrahim Inga, ya ce akalla gidaje hudu ne suka saukar da masu gudun hijira a garin.
Ya ce wuraren su ne: Three arm zone, mutum 248; Bayan Dana, 68; FM Junction, 48; Angwan Daaji, 59
An kuma gano cewa Hukumar na shirin mayar wa wasu Fulani ’yan gudun hijirar zuwa sansanin ’yan gudun hijira da ke Sarkin Pawa.
A lokacin da ya ziyarci sansanin ’yan gudn hijirar da ke Minna, Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya zargi Gwamnatin Tarayya da yin shakulatun-bangaro da halin da mutanen suke ciki.