✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fulani ku guji bata aikin Shugaba Buhari – Oba Gbadebo III

Babban basaraken Lardin Egba a Jihar Ogun Oba Adedotun Aremu Gbadebo III ya gargadi Fulani makiyaya da su guji bata kyawawan ayyukan cigaban kasa wadanda…

Babban basaraken Lardin Egba a Jihar Ogun Oba Adedotun Aremu Gbadebo III ya gargadi Fulani makiyaya da su guji bata kyawawan ayyukan cigaban kasa wadanda Shugaba Buhari ya tanadar wa kasar nan a zangon mulkinsa.

Alaken na Lardin Egba ya yi gargadin ne a lokacin da tawagar shugabannin kungiyar Fulani makiyaya ta Miyatti Allah na kasa da sarakunan Fulani suka kai ziyarar bangirna a fadarsa da ke Abekuta.
A cewar Oba Adedotun tun a lokacin da yake aikin soji a rundunar sojin Najeriya yasan kowane ne Shugaba Buhari. Don ya yi aiki a karkashin sa, yasan shi da tsayuwarsa bisa gaskiya da rikon amana da jajurcewa da son wanzar da zaman lafiya. Don haka ya ja hankulan Fulani makiyayan da su guji tayar da tarzoma tsakaninsu da manoma, ta hanyar yi wa manoma barna domin a cewarsa, yin haka barazana ce ga kyawawan kudirorin Shugaba Buhari, musanman ma yunkurin sa na bunkasa harkar noma a kasar nan.
Alaken ya nuna farin cikin sa da yadda shugabanin ƙungiyar Fulani makiyaya suka hada kai da ’yan uwansu na ƙungiyoyin manoma suke aiki tukuru, domin wanzar da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin su.
Ya ce wannan abu ne mai matukar mahimmanci, domin ko a kwanakin baya ma ya halarci taro makamancin haka a Jihar Kaduna, inda bayanai suka nuna cewa, da yawa daga cikin Fulanin da suke tayar da tarzoma ba ’yan Najeriya ba ne. Don haka ya yi kira ga jami’an kula da shige da fice na kasar nan da su sanya ido sossai, domin tabbatar da cewa wasu mutane ba sa shigowa ta haramtattun hanyoyi, suna zuwa suna haddasa tarzoma a kasar nan.
Ya ce kyawawar alakar da aka samu a tsakanin kungiyoyin manoma da makiyaya a Jihar Ogun abu ne mai kyau, domin haka ya taimaka kwarai wajen magance rigingimu.
“Ai dama can bai dace ba daga an samu baraka dabobbi sun yi barna a gona abin ya kai ga tashin hankali. barna ce da idan ta riga ta faru za a zauna a tattauna yadda za a magance matsalar,” inji shi wanda a ƙarshe yayi addu’ar ɗaurewar kyakyawar alaƙar da ke tsakanin makiyaya da manoman jihar.
Tawargar shugabannin kungiyar Fulani makiyaya ta miyatti Allah a karkashin jagorancin shugabanta na kasa Alhaji Muhammadu Kiruwa Hardon Zuru, sun kai ziyarar aikin gani da ido a Jihar Ogun, inda suka shafe yini biyu suna taruruka tsakanin su da sarakunan Fulanin jihar da jihohin da ke makwaftaka da ita. Bayan wani zama da suka yi da kungiyar manoman jihar a kan maganar shiga makiyayar Iguwa bisa tsare-tsaren da ya kamata a yi don guje wa aukuwar tashin hankali da ka iya janyo salwantar rayuka a tsakanin Fulani makiyaya da manoma kamar yadda aka saba gani a baya.
A zaman da ƙungiyar miyatti Allah ta yi da ƙungiyoyin manoman, shuwagabannin manoman sun nuna rashin jin daɗin su ganin yadda filanin suka karya yarjeje niyar da aka ƙulla don shiga makiyayar Iguwa, inda aka ware ranar 27 ga watan Disamban nan a matsayin ranar da fulani zasu soma shiga makiyayar amma sai wasunsu suka ƙeƙa ƙasa suka yi watsi da yarjejeniyar suka shiga makiyayar tun a farkon watan da ya gabata.
Shugaban ƙungiyar ta filani makiyaya Alhaji Muhammadu Kirwa Hardon Zuru, ya shaida wa Aminiya cewa, makasudun zuwan su shi ne daidaita tsakanin manoma da makiyaya, musanmman a bangaren makiyayar Iguwa, don ganin a bana ba a samu wani rikici ba domin ya baya an samu salwantar rayuka a wajen.
Ya ce a kwanakin baya ma sun yi irin wannan taro a Jihar Enugu, tare da daukacin shugabanin kungiyar na jihohin Najeriya. Kuma kungiyar za ta ci gaba da bibiyar duk inda ake da wata matsalar a tsakanin makiyaya da manoma don daidaita tsakani.
kungiyar ta bai wa masu laifukan da suka hada da satar shanu da garkuwa da mutane damar su fito su tuba, inda mutum biyu suka bayyana kansu suka tuba aka rantsar da su da Alkur’ani mai girma.