✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

FSARS: Masu zanga-zanga sun mamaye hedikwatar ’yan sanda

Suna neman a rushe rundunar yan sanda ta FSARS da ake zargi da kama-karya

Masu zanga-zanga neman a rushe rundunar ’yan sanda ta FSARS mai yaki da ayyukan fashi sun mamaye Hedikwatar ’Yan Sanda ta Kasa da ke Abuja.

Masu zanga-zangar sun yi zaman dirshen tare da mamaye titin Shehu Shagari da ke birnin Abuja, suna wake-wake tare da daga kwalaye masu kira da a rusa FSARS.

Wakilinmu ya gan su suna zane-zane da jan fenti domin alamta kashe-kashen da ake zargin jami’an rundunar da aikatawa.

Zuwa lokacin da aka aiko da wannan rahoto babu wani jami’in rundunar da ya je domin yi wa masu zanga-znagar jawabi.