✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

#FreeAminu: NANS ta kira zanga-zangar adawa da Aisha Buhari

NANS ta ce an keta haddinsa dalibin.

Kungiyar Daliban Najeriya (NANS) ta yi tir da tsare Aminu Adamu bisa zargin bata sunan uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari.

Shugaban NANS, Usman Barambu, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya bukaci a sako dalibin na Jami’ar Tarayya ta Dutse ba tare da bata lokaci ba.

Ya kuma ba da sanarwar gudanar da zanga-zanga a fadin Najeriya a ranar Litinin, 5 ga watan Disamba, 2022 don ganin an saki dalibin.

“Sakamakon kama daya daga cikinmu da jami’an gwamnati suka yi ba bisa ka’ida ba tare da azabtar da shi, kungiyar NANS za ta gudanar da zanga-zanga.

“Za mu yi zanga-zanga a fadin Najeriya daga ranar Litinin 5 ga Disamba, 2022 ne don neman ’yancin Aminu Adamu Muhammed, dalibin Jami’ar Tarayya ta Dutse.”

Barambu ya ce za a yi zanga-zangar ce domin adawa da uwargidan shugaban kasa da kuma shugaban ’yan sanda Usman Baba, kan cin zarafi da tauye hakkin dalibin.

Aminu, wanda dalibin ajin shekarar karshe ne a Sashen Nazarin Muhalli a jami’a, na fuskantar tuhuma kan yin batanci ga uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari.

An gurfanar da shi a kotu, inda Mai Shari’a Halilu Yusuf na Babbar Kotun Birnin Tarayya, ta tisa keyarsa zuwa gidan yarin Suleja da ke Jihar Neja bisa zargin aikata cin zarafi a intanet.

Tsare dalibin ya janyo ce-ce-ku-ce a kafofin sada zumunta, inda dubban mutane ke kira da a sake shi.

Hakazalika, kungiyar kare hakkin bil-Adama ta duniya (Amnesty International) ta bukaci a gaggauta sakin dalibin.