✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

FMC Katsina za ta koma Asibitin Koyarwan Jami’ar Umaru Musa

Gwamnatin Tarayya ta amince da daga darajar Cibiyar Lafiya ta Tarayya (FMC) da ke Jihar Katsina zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Umaru Musa Yar’Adua. Amincewar…

Gwamnatin Tarayya ta amince da daga darajar Cibiyar Lafiya ta Tarayya (FMC) da ke Jihar Katsina zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Umaru Musa Yar’Adua.

Amincewar ta biyo bayan yarjejeniyar fahimtar juna da Gwamnatin jihar Katsina ta kulla da Gwamnatin Tarayya suka sa wa hannu ranar Talata.

Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari ne ya sanya hannu a yarjejeniyar a madadin jihar yayin da Ministan Lafiya, Osagie Emmanuel Ehanire ya sanya hannu a madadin Gwamnatin Tarayya.

Mahalarta taron sun hada da Minista a ma’ikatar lafiya, Olurunimbe Mamora da babban Sakatare a ma’aikatar, AbdulAzeez Abdullahi Mashi da darakta a Asibitin Kwararru na Jihar Katsina, Dokta Suleiman Bello Muhammad.

Sauran sun hada da mai ba Gwamnan Katsina shawara a fannin makarantun gaba da sakandare, Bashir Muhammad Ruwan Godiya da Shugaban Jami’ar Umaru Musa Yar’Adua, Farfesa Sanusi Mamman, da sauran manyan jami’an Gwamnatin Tarayya da Jihar Katsina.