Kowace shekara kan zo ta kuma kare tattare da abubuwa masu yawa na yabo da ban al’ajabi da takaici da sauransu.
Shekara mai karewa ta 2022 ita ma cike take da al’amura da suka auku wadanda tarihi ba zai manta da su ba.
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Kamata Ku Sani Kan Ranar Kyauta A Addinin Kirista
- Dalilin da zan koma Daura idan na bar mulki —Buhari
Daga cikin muhimman abubuwan da suka auku a 2022, Aminiya ta kalato muku bangaren yadda mutunci da kimar wasu fitattun mutane suka samu alamar tambaya sakamakon tsare su da aka yi kan aikata ba daidai ba.
Daga cikin wadannan mutanen akwai:
DCP Abba Kyari
DCP Abba Kyari na daga cikin wadanda Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), ta tsare ta kuma gurfanar da shi a kotu bisa zarginsa da hannu a safarar miyagun kwayoyi na biliyoyin Naira.
Duk da dai badakalar Kyari ta fara ne tun a 2021, amma sai 2022 aka tsare shi.
Lamarin tsare Kyari ya jefa dimbin ’yan kasa cikin tunani da mamaki, la’akari da cewa dan sanda ne da ake yaba kwazonsa wajen yaki da masu aikata manyan laifuffuka, sai ga shi ana zarginsa da aikata laifin da ake ganin ba zai sa kyale duk wanda ya kama ya aikata ba.
Ko shakka babu, wannan ya taba mutunci da kimar Kyari a idon duniya.
Rochas Okorocha
Daga cikin wadanda suka yi wasan buya da hukumar EFCC a 2022, har da tsohon Gwamnan Jihar Imo kuma Sanatan Imo ta Yamma a Majalisar Tarayya, Rochas Okorocha.
EFCC ta tsare shi ne kan zargin karkatar da kudi da kadarorin Jihar, lokacin yana Gwamna na kimanin Naira biliyan 2.9.
Jami’an hukumar sun kai wa tsohon Gwamnan samame ne a gidansa na Abuja inda suka kama shi.
An bi sahunsa har gida ne saboda kin amsar gayyatar da hukumar ta yi masa tun farko cikin lalama.
Tsohon Akanta-Janar, Ahmed Idris
EFCC ta yi dirar mikiya a kan tsohon Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris a ranar 16 ga watan Mayu, 2022 bisa zargin yin sama da fadi da dukiyar gwamnati kimanin Naira biliyan 80, inda aka ce ya yi amfani da ‘yan uwa da wasu makusanta wajen tafka almundahana.
Sai dai daga bisani an ce kudin da ake zarginsa da kaekatarwar sun kai Naira biliyan 170.
Hakan dai ya sa an dakatar da shi daga mukaminsa, kafin daga bisani kuma EFCC ta maka shi a gaban kotu.
Tsohon Gwamnan Anambra, Obiano
Haka shi ma tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Willie Obiano, bai tsira ba. Domin kuwa, a watan Maris, 2022 EFCC ta tsare shi kan zargin karkatar da kudaden Jihar Anambra wajen kashe wutar gabansa.
EFCC ta cafke shi ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas, lokacin da yake kokarin barin kasa jim kadan da mika mulki ga sabon Gwamnan Anambra, Farfesa Charles Soludo.
Tsohon Gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari
Tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ma an taba kimarsa bayan da EFCC ta tsare shi a watan Mayu, 2022 kan zargin amfana da kason Naira biliyan 22 da aka ce ya yi daga biliyan N84 da ake zargin tsohon Akanta Janar, Ahmed Idris da karkatarwa.
Tsohuwar Kakakin Majalisar Wakilai
Tsohuwar Shugabar Majalisar Wakilan Najeriya, Patricia Etteh, na daga cikin wadanda ake musu kallon girma ya fadi a 2022, kasancewar ita ma EFCC ta damke ta ran 17 ga Mayu kan dalili mai alaka da tafka magudi a kwangilar miliyan N130 da aka bayar don kafa fitilun kan tituna masu amfani da hasken rana a Jihar Akwa Ibom.