✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Fitaccen mai yaki da ‘yan fashi, Ali Kwara ya rasu

Shahararen mai kama barayin nan a Arewacin Najeriya, Alhaji Ali Ƙwara Azare ya rasu.

Shahararren mai kama barayin nan a Arewacin Najeriya, Alhaji Ali Ƙwara Azare ya rasu.

Ya rasu ne ranar Juma’a 6 ga watan Nuwamba a Abuja bayan ya sha fama da jinya.

Marigayin Ali Kwara dai ya shahara a ‘yan shekarun bayan wajen yaki da bata-gari musamman ‘yan fashi da makami.

Ya kan ladabtar da barayin ta hanyar koya musu sana’o’i bayan kama su.

Dan asalin garin Azare na karamar hukumar Katagum a jihar Bauchi, marigayi Ali Kwara ya rasu ya bar mata da ‘ya’ya.