✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Firaiministan Pakistan ya shiga dakin da aka binne Manzon Allah a Madina

An bai wa Imran Khan da matarsa damar shiga dakin da aka binne Fiyayyen Halitta.

Mahukunta Masallatan Alfarma na Saudiyya, sun bai wa Firaiministan Pakistan Imran Khan, damar shiga dakin da aka binne Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad (SAW) a masallacinsa da ke birnin Madina.

Shafin mahukuntan mai suna Haramai Sharifain ne ya bayyana hakan tare da hotunan Firaiministan cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

An bude wa Firaiministan tare da matarsa dakin da kabarin Manzon Tsiran yake yayin da suka ziyarci masallacin a ranar Lahadi.

Kazalika, a cikin dakin ne kuma akwai kaburburan Sahabbai biyu mafi falala na Manzon suke, wato Sayyadina Abu Bakr bn Saddiq da kuma Umar bn Khaddab, aminci ya kara tabbata a gare su.

Ingatattun tarihi sun bayyana cewa, bayan wafatin Manzon Allah, an binne shi ne a dakin matarsa, Nana Aisha RA, inda ya yi jinyarsa ta ajali kamar yadda al’ada ta tanadar na binne duk wani Annabi a inda ya rasu.

Kazalika, an binne halifofin biyu na Manzon Allah a kusa da kabarinsa bayan sun nemi alfarmar hakan daga wurin Nana Aisha.

Imran Khan da mai dakinsa tare da tawagar mahukuntan Saudiyya a masallacin Annabi
Imran Khan da mai dakinsa a masallacin Annabi da ke Madina
Imran Khan yayin fitowarsa daga dakin da aka binne Manzon Allah