Rashin lafiya ya sa Firai Ministan kasar Japan, Shinzo Abe, ya yi murabus babu shiri.
Abe ya yi bayanin cewa ba ya so ko kadan rashin lafiyarsa ya yi tasiri wajen kawo nakasu a aikinsa da ya shafi riko da akalar jagorancin kasar cikin inganci.
A dalilin haka ne Mista Abe ya ke neman al’ummar kasar da su yi hakuri da gazawarsa wajen karasa wa’adin mulkinsa.
Shinzo Abe, wanda ya shekara 65 a duniya, ya dade yana fama da cutar gyambon ciki wadda ta yi wa hanjinsa rikon kazar kuku, ya kuma ce a yanzu radadin ciwon ya kara tsanani.
An kirkiri Masallacin tafi da gidanka a Japan
Ko Zaben Abe Zai Kawo Sauyi Kan Rigimar Amurka Da Koriya Ta Arewa?
A bara dai ya kasance Firai Ministan kasar Japan wanda ya fi kowanne dadewa a kan gadon mulki wanda ya dare kansa tun a shekarar 2012.
Shafin intanet na BBC ya ruwaito cewa Mista Abe zai ci gaba da mulki har zuwa lokacin da za a zabi sabon Farai Ministan da zai maye gurbinsa.