Fiame Naomi Mata’afa, wadda ita ce tsohuwar Mataimakiyar Firai Minista a kasar ta Samoa, ta fara aiki ne a ranar Talata, inda ta dare kan kujerar tsohon ubangidanta Tuilaepa Sailele Malielegaoi, wanda ya yafe shekara 22 a matsayin Firai Minista, ya kuma yi yunkurin hana ta mulki.
Tuni Fiame mai shekara 64 ta jagoranci zaman farko na Majalisar Ministocin jam’iyyarta ta FAST, ta kuma sanar cewa a shirye suke tsaf su fara aiki.
Manyan ayyukan da ke gaban sabuwar Firai Ministan sun hada da batun kyautata dangantaka tsakanin kasarta ta China.
Sai dai kuma a lokacin yakin neman zabe ta yi alkawari soke aikin bunkasa tashar jirgin ruwa na Dala miliyan 100 da China take goyon baya a Samoa, bisa hujjar aikin zai kara matsa wa tattalin arzikin kasar da dama can China na bin ta basussuka masu yawan gaske.
An ki ba ta mulki
Bayan lashe zabe a watan Afrilu, Firai Minista Tuilaepa Sailele Malielegaoi ya ki amincewa da shan kaye a hannun Fiame, duk da cewa kotuna daban-daban sun tabbatar da nasarar abokiyar karawar tasa.
A lokacin, manyan na hannun daman Mista Tuilaepa, Shugaban Kasa da kuma Shugaban Majalisar Dokoki sun yi kokarin hana mika wa Fiame mulki.
A watan Mayu an hana Fiame da ’yan jam’iyyarta shiga zauren Majalisar kasar, a yayin da ikirarin cewa shi ne halastaccen Firai Minista. Bangarorin biyu sun zargi juna da yunkurin juyin mulki.
A lokacin ne Firai Minista Fiame da ’ya’yan jam’iyyarta suka karbi rantsuwar kama aiki tare da nada ministoci a wani karamin taro da aka yi a karkashin wata rumfa a gaban ginin majalisar da ke rufe.
A wata hira da aka yi da ita, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa, hankalinsu ya tashi a ranar, “Da abubuwa sun lalace, amma muka kai zuciya nesa.”
“Ba don haka ba da mun shiga mun babballa kofofin kamar yadda aka yi a Washington, D.C. Amma muka yi zaman dirshen muna wake-wake da addu’o’i.”
A makon jiya Kotun Kolin Samoa ta yanke hukunci da ke tabbatar da tabbatar da rantsuwar a aka yi wa Firai Minista Fiam wajen Majalisar a matsayi halastacce, daga baya Tuilaepa ya sallama.
Yadda Fiame da Tuilaepa suka raba jiha
A cikin hirar da aka yi da ita, ta ce ta yi murabus ne bayan da ta damu matuka cewa Tuilaepa da takwarorinsa ’yan majalisa sun “sauka daga kan layi” ta hanyar kokarin yin katsalandan a tsarin kotunan kasar da kuma bangaren shari’a.
Fiame ta ce, “Muna ta zamewa daga bin doka, kuma ba na son hakan. Amma yawancin ’yan jam’iyya sun yarda da abin da ake yi.”
Ta ce Tuilaepa bai taba tunanin zai iya faduwa zabe ba, musamman ganin yadda yake da rinjaye a majalisar.
“Ya kadu matuka, har ya kasa gaskata abin da ya faru,” inji ta.
Ana ganin nasarar zaben Fiame a matsayin babban cigaba ba kawai ga Samoa ba, wanda ke da ra’ayin mazan jiya, har ma da yankin Kudancin Pacific, wanda ke da shugabanni mata kadan.
Fiame ta ce ba ta tsammanin jinsinta babban lamari ne a zaben, kuma rawar da ta taka a tsarin mulki na iya zama mafi mahimmanci ga masu jefa kuri’a.
Amma ta yi fatan cewa ta iya zama kyakkyawan abin koyi ga matan Pacific a wasu fannoni sa suke nem cimma burinsu.