✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fintiri ya tsallake rijiya da baya a wani hatsarin ayarin motocinsa

Karo na biyu a cikin kasa da mako guda da gwamnan ke tsallake rijiya da baya a hatsarin mota

Rahotanni sun bayyana cewa Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya tsalkake rijiya da baya, yayin da mutum hudu suka mutu sakamakon hatsari da ayarin motocinsa suka yi a kan hanyarsu ta zuwa Mubi domin gudanar da yakin neman zabe.

Wata majiya ta ce hatsarin ya yi ajalin mutum uku nan take, na hudun kuma ya cika a lokacin da aka kai shi asibiti don ceto rayuwarsa.

Wasu mutum biyar sun samu raunuka kuma tuni aka garzaya da su asibiti, inda ake duba lafiyarsu, bayan aukuwar hatsarin a kusa da Fadamareke da ke Karamar Hukumar Hong ta jihar.

An ajiye gawarwakin mutum uku daga cikin wadanda suka mutu a wani asibiti da ba a bayyana ba.

Gwamna Ahmadu Fintiri, wanda da shi aka yi ta kokarin ceto wadanda hatsarin ya rutsa da su, ya bayyana damuwa matuka, tare da mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka mutu.

A makon da ya gabata ne dai Gwamna Fintiri ya tsallake rijiya da baya, bayan wata babbar motar dakon kaya ta kusa kutsawa cikin ayarin motocinsa da ke tsaye.

Lamarin ya faru ne a kusa da Masallacin Dougirei da ke tsaunin Agga, inda gwamnan ya je halartar daurin aure.

’Yan sanda biyu da suka samu munanan raunuka sakamakon hatsarin, an garzaya da su sashen kula da hatsarid a tsautsayi na asibitin kwararru da ke jihar.