✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Finidi George ya zama Babban Kocin Super Eagles

A watanni biyu da suka gabata George ya jagoranci Super Eagles a sawannin zumunci biyu a kasar Morocco, inda a wasan farko suka lallasa Ghana…

Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) ta nada Finidi George a matsayin Babban Kocin babbar tawagar ’yan wasan Super Eagles.

Kakakin NFF, Ademola Olajire, ne ya fitar da sanarwar a ranar Litinin cewa Finidi George ne zai ci gaba da jan ragamar horar da Super Eagles.

George wanda tsohon dan wasan Super Eagles ne, ya shafe watanni 20 a matsayin mataimakin tsohon babban kocin kungiyar, José Peseiro, wanda ya jagorance su suka lashe kambin azurfa a Gasar Nahiyar Afirka (AFCON 2023) a kasar Kwaddibuwa.

Jin kadan da kammala gasar AFCON 2023 Peseiro dan kasar Portugal ya yi murabus don kashin kansa, daga nan Finidi George ya ci gaba da horas da ’yan wasan a matsayin riko.

A watanni biyu da suka gabata George ya jagoranci Super Eagles a sawannin zumunci biyu a kasar Morocco, inda a wasan farko suka lallasa Ghana da ci 2-1, wanda ya kawo karshe shekaru 18 a jere da Ghana ke doke su.

Sai dai kuma Super Eagles din sun sha kashi da ci 2-0 a hannun kasar Mali.

Finidi George na cikin tawagar ’yan wasan Najeriya da suka lashe gasar AFCON 1994 a kasar Tunisia.

Su ne kuma suka zama na biyu wajen kayatar da masu kallo a gasar Kofin Duniya a 1994 a kasar Amurka, wanda shi ne karon farko da Najeriya ta buga gasar Kofin Duniya.

Sabon kocin na Super Eagles ya ci wa Najeriya kwallaye 63, sannan ya sau biyu yana zuwa wasan karshe a Gasar Kofin Duniya, a 1994 da 1998.

A shekarun 1992, 1994 da 2000 ya samu kambunan zinare azurfa da tagulla a gasannin AFCON.

Kwallon Finidi George ta farko a Gasar AFCON ita ce wadda ya zura a wasan Najeriya da Burkina Faso a Babban Filin Wasa na Kasa da ke Legas a 1991.

Shi ne kuma ya taimaka wa marigayi Rashidi Yekini cin kwallon Najeriya na farko a gasar Kofin Duniya a 1994, a wasansu da kasar Bulgaria a Amurka.

Sannan shi ne dan wasan da ya zura kwallon da ya kai Najeriya ga gasar wanda shi ne karon farko da Super Eagles suka shiga gasar cin kofin Duniya.

A nan gida kuma tsohon dan wasan Calabar Rovers da Sharks FC ne kafin ya samu damar zuwa Turai.

Babban aikin da ke gabansa shi ne sama wa Super Eagles gurbi a kasar Kofin Duniya na 2026, ta hanyar yin nasara a wasanninsu da kasahen Afirka ta Kudu da kuma Jamhuriyar Benin a nan da kimanin makonni biyar masu zuwa.