✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Filin kwallon da jirgin kasa ke bi ana tsaka da wasa

To wannan labarin ba almara ba ce, gaske ne

Shin yaya za ka ji idan kana tsakiyar kallon kafa cikin filin wasa, Sai kungiyarka na daf zura kwallo a raga abokiyar karawarta hankalinku duk ya tafi kan yadda za ci kwallon sai kawai ka ji karar jirgin kasa ya kuma zo ya wuce ta gabanka a inda kake zaune a rumfar ‘yan kallo?

Wannan ba almara ba ce, hakan abin yake a filin wasan kwallon kafa mai suna Clerny Balog na kungiyar kwallon kafa ta TJ Tattran da ke kasar Slobakia. Inda hanyar jirgin kasa ya ratsa ta cikin filin wasan kuma daf da rumfar ‘yan kallo wanda hakan ya cigaba da daukar hankalin mutane a duniya.

A cewar jaridar Independent ta Ingila, wucewar jirgin ana tsaka da wasan kwallo ba ya shafar wasannin da ake yi, bai kuma taba hargitsa wa ‘yan wasa ko kallo al’amarinsu na wasa ba ko kuma katsewa ‘yan kallo jin dadin wasansu ba.

A maimakon haka ma wucewar jirgin ana wasa wani abin mamaaki ne da sha’awa ga ‘yan kallo musanman farkon zuwa.

Rahotanni na cewa an gina filin wasan na Clerny Balog ne cikin shekarun 1980 a zamanin tsohuwar hukumar kula zirgazirgar jiragen kasa ta kasar.

Sai dai babu wasu cikakkun bayani na dalilin da hukumar kula da raya birane ta kasaar ta yanke sha’awar gina hanyar jirgin ya kuma ratsa ta cikin filin wasan.

Kasancewar an daina amfani da irin wadannan jiragen kuma tsawon wadannan shekaru an bar hanyar jirgin tamkar wani abin ado a filin wasan ba tare an ciresu ba, ko wani abu makamancin haka.

Amma a farko shekarun 1990 wasu masu sha’awar harkar jiragen kasa suka gyara hanyar jirgin.

A kuma shekarar 1992 aka bude hanyar layin dogon domin soma amfani da shi a hukumance a matsayin wani abin kuzo-ku-gani na tarihi musamman ga ‘yan yawon bude ido.

Tun daga lokacin kuma jiragen irin na da, masu amfani da kwal ke kai komo a layin dogon, wasu lokutan ana tsaka da wasan kwallon kafa na kungiyar.

An yi itifakin cewa filin wasan na Cleeny Balog shine fili guda daya tilo a duniya wanda layin dogo na jirgin kasa ya wuce ta cikinsa wanda kuma ana amfani da shi, a inda ana tsaka da wasa kuma jirgi na wucewa babu ruwnan kowa da shi duk da karar wucewarsa da kuma ihunsa.

A lokuta da yawa na cikin jirgin ne da kuma ‘yan a kallon wasa da ke waje, ke yiwa juna adabo cikin raha da murna da kuma farin cikin wannan abin mamaki.