A sakamakon zaman dardar da ake ciki a Karamar Hukumar Mangu da ke Jihar Filato. Shugaban Karamar Hukumar, Markus Artu, ya sanya dokar hana zirga–zirga ta tsawon awa 24.
Shugaban ya sanya dokar ce a wata sanarwa da ya fitar mai dauke da sanya hanunsa., ranar Litinin.
- Za a shafe kwana 3 ana ruwan sama da tsawa a Jihohin Arewa
- Za a tada ganuwar Kano da ɓuraguzan rusau
Sanarwar ta yi bayanin cewa dokar ta kunshi hana zirga-zirgar dukkan ababen hawa na awa 24 a yankin, har sai abin da hali ya yi.
“Ba a son ganin kowa yana zirga-zirga a yankin, sai dai jami’an tsaro ko kuma wadanda aikinsu ya zama wajibi ga al’umma,” in ji sanarwar.
Matakin sanya dokar na zuwa ne bayan da aka sami wasu munanan hare-hare kwanakin baya.
Hare-haren dai sun yi sanadin asarar rayukan sama da mutum 150 da dukiyoyi masu tarin yawa.