Hukumar shirya wasan kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta soke wasan sada zumunci a tsakanin Najeriya da Ghana wanda aka so yi a wannan watan a Landan.
Hukumar ta ce ta soke wasan ne saboda ya saba wa ka’idar hukumar na wata kasa ta yi wasan sada zumunta da wata kasa a tsakanin kwanaki uku, kamar yadda kundin tsarin hukumar FIFA ya tanadar.
Najeriya za ta yi wasan sada zumunta ne da Bolibiya a ranar 26 ga wannan wata ne sannan ta gayyaci Ghana kuma don yin wasan sada zumunta a ranar 29 ga wannan wata, watau a tsakanin kwanaki uku kacal.
Da wannan soke wasan da hukumar FIFA ta yi, Ghana tana iya yin wasa da duk kasar da ta neme ta da yin haka, tun da an soke na Najeriya da Ghana.
Idan za a tuna Ghana ce ta zama ta biyu a gasar cin kofin Afirka da ya gudana a Ekuatorial Guinea inda Kwaddebuwa ta doke ta a wasan karshe a bugun fanariti da ci 9-8.
Najeriya ta shirya wasannin sada zumunta ne a shirye-shiryen tunkarar gasar cin kofin Afirka na shekarar 2017.