✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

FiFA ta ci tarar Senegal kan haske Salah da fitila

FIFA ta ci Senegal tarar kudi dala 180,000 kan haske idon Salah yayin bugun fenariti.

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA), ta ci tarar Senegal dalar Amurka 180,000 kan yadda magoya bayanta suka haska fuskar dan wasan Masar Mohamed Salah da fitila yayin bugun fenariti a wani wasan fitar da gwani na Gasar Kofin Duniya

Baya ga tarar da FIFA ta Senegal, ta sake kakaba mata takunkumin buga wasa daya a gida ba tare sa magoya bayanta ba.

A watan Maris da ya gabata ne Salah ya yi yunkurin buga fenariti a wasan da Senegal da Masar suka gwabza, wanda magoya baya suka haske masa ido da fitila, lamarin da ya yi sanadin gaza zura kwallon a raga.

A watan Janairu Masar ta yi rashin nasara a wasan karshe na gasar kofin nahiyar Afirka (AFCON) a hannun Senegal a bugun fenariti.

Kazalika, FIFA ta sake cin Senegal tara kan gaza samar da cikakken tsaro kan yadda magoya baya suka dinga bayyana alluna masu dauke da rubutun cin zarafi da munanan kalamai ga ‘yan kwallon Masar, wanda hakan ya ci karo da sashe na 16 na kundin laifukan FIFA.

%d bloggers like this: