✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fetur zai wadata a ƙarshen mako —Minista

Ƙarin kuɗin man ya haddasa tashin farashin kayayyaki a faɗin Najeriya

Ministan Man Fetur, Heineken Lokpobiri, ya ba wa ’yan Najeriya tabbacin cewa daga wannan karshen makon za a samu wadataccen man a faɗin ƙasar.

Wannan na zuwa ne bayan ƙarin kuɗin man fetur ya haddasa tashin farashin kayayyakin masarufi da na sufuri a faɗin ƙasar.

Lokpobiri ya bayar da tabbacin ne bayan zaman gaggawa kan matsalar man fetur ɗin da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya gana da shi da Shugaban Kamfanin NNPC, Mele Kyari da Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu.

Ministan ya ce Shettima ya kira zaman ne bisa umarnin Shugaba Tinubu saboda damuwarsa da matsalar da rashin man ta jefa al’ummar Najeriya a ciki.

A baya-bayan nan ne dai NNPC ya yi wani karin kudin mai na hudu a wani yanayi mai cike da ruɗani.

An kuma samu dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai a fadin ƙasar a sakamakon ƙarancin man.

A ranar Laraba da Alhamis Aminiya ta lura gidajen man NNPC na sayar da litar fetur a kan N897 zuwa N950, ya danganci inda suke a faɗin Najeriya.

Kafin nan amkan N568-N617 gidajen man na NNPC suke sayar da kowace lita.

A halin yanzu dai gidajen man ’yan kasuwa na sayar da lita a kan N930 zuwa N1,400, masu bumburutu kuma na sayarwa a kan 1,100 zuwa N1,500.

Tuni dai al’ummar ƙasar da kungiyar kwadago suka koka kan sabon ƙarin kuɗin man tare kira da a gaggauta janye shi.

Ƙungiyar masana’antu da kasuwanci (MAN da NACCIMA) sun bayyana cewa ƙarin kuɗin man zai ƙara tsananta tsadar kayayyaki a ƙasar wanda hakan babban barazana ce ga yanayin rayuwar al’umma da ma kamfanoni.

Amma da yake jawabi, Minista Lokpobiri ya ce gwamnati ba ta sanya farashin da za sayar da man, saboda ta riga ta janye hannunta, kamar yadda dokar man fetur ta PIA ta tanada.

Ya kuma bukaci al’umma da su daina sayen man da fargabar za a ci gaba da ƙarancinsa, inda ya ba da tabbacin cewa daga ƙarshen mako man zai wadatu.

Sayen man Matatar Dangote

Wata sanarwa da kamfanin NNPC ya fitar ta ce yanayin kasuwa da farashin musayar kuɗaɗen ƙasashen waje ne ke yin alƙalanci kan yadda farashin mai ke kasancewa.

Game da fara dakon man fetur daga Matatar Ɗangote kuwa, sanarwar da kakakin NNPC, Olufemi Soneye, ya sanya wa hannu ta ce sai ranar 15 ga watan Satumba da Matatar Ɗangote ta ba su za a fara.

Farashin kaya ya tashi

Binciken Aminiya ya gano cewa farashin kayan abinci ya tashi a kasuwanni a sakamakon ƙarin kuɗin man.

A kasuwannin Abuja, an samu ƙarin akalla N200 a kan kowane kwano guda ma kayan hatsi, a sakamakon ƙarin kuɗin man.

A ranar Laraba, karin kuɗin man ya jawo ƙaruwar kudin ababen hawa na haya da kashi 50% a fadin ƙasar.

Ma’aikatan gwamnati da sauran masu sayayya dai na kokawa da hauhawar farashin.

Kano

A kasuwannin Kano kuma, bugun wake ya kara kuɗi daga N190,000 zuwa N200,000 a Kasuwar Hatsi ta Dawanau

A kasuwar kayan tireda ta Singa kuma kudin kwalin taliya ya karu da N1,500.

Buhun shinkafar gida ya karu da N12,000. Buhun 50kg na shinkafa kuma ya karu da N5,000, buhun gari kwaki kuma ya ƙaru da N8,000.

Kaduna

Babban buhun shinkafa a kasuwannin Kaduna ya karu da N7,000, dawa ta karu da N2,000, wake ya karu fa N10,000, kwalin taliya kuma ya karu da N2,0000.

Bauchi

A Bauchi ma buhun shinkafa ya tashi da N5,000, kwandon tumatir ya karu da N4,000 sai tattasai da ya kara N8,000