✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

FCMB da Gidauniya sun ɗauki nauyin yi wa mutum 150,000 aikin ido a Kebbi

Bankin ya ce zai ci gaba da taimaka wa rayuwar al'umma musamman mazauna karkara.

Bankin FCMB tare da haɗin gwiwar Gidauniyar Tulsi Chanrai, sun ɗauki nauyin yi wa aƙalla mutum 150,000 aikin ido kyauta a Jihar Kebbi.

Tallafin, wanda aka fara a shekarar 2009, na da nufin taimaka wa waɗanda ke fama da matsalolin ido a dukkanin ƙananan hukumomi 21 da ke jihar.

A wajen taron bikin murnar cikar shirin shekara 15 da kafuwa, wanda aka yi a Birnin-Kebbi, matar Gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya Nafisa Idris, ta gode wa FCMB bisa ƙoƙarinsa na daƙile makanta a tsakanin mutane.

“Muna godiya ga FCMB da Gidauniyar Tulsi Chanrai saboda taimaka wa mutane da ke fama da matsalolin ido. Wannan taimakon yana faranta ran mutane ta hanyar sake gudanar da rayuwa cikin farin ciki,” in ji ta.

Shugaban Sashen Hulɗa da Jama’a na FCMB, Diran Olojo, ya bayyana cewa bankin ya ƙuduri aniyar gina al’umma ta hanyar bayar da tallafi irin wannan.

Ya bayyana cewa mutane sama da mutum 400,000 a jihohi daban-daban na Najeriya ne, suka amfana da shirin tun da aka fara shi.

Wani daga cikin waɗanda suka amfana, Muhammad Maganda, ya nuna godiyarsa bayan yi masa aiki kyauta wanda hakan ya taimaka ganinsa ya dawo.

Mutumin, ya ce hakan ya ba shi damar komawa gona domin ci gaba da al’amuransa kamar yadda ya saba a baya.

“Na kusa rasa idona kuma na ji tsoro, amma yanzu ganina ya dawo kuma ina iya aiki. Ina matuƙar godiya,” in ji shi.

Wata mata da ci gajiyar shirin, Fatima Abdullahi, ta bayyana farin cikinta bayan dawowar ganinta, kuma ta gode wa FCMB kan yadda aka mata aiki kyauta.

“Ganina da rayuwata sun dawo. Duk abin da aka min na magani da aiki kyauta ne. Ba ni da kalmomin da zan yi amfani da su wajen bayyana farin cikina. Allah Ya yi FCMB albarka kan taimakona, na dawo yin rayuwata daidai da kowa.”

Bankin ya ce zai ci gaba da ƙoƙari wajen daƙile makanta musamman wanda za a iya yi wa magani tare da inganta rayuwar mutane a faɗin ƙasar nan.