kungiyoyi 16 ne suka fafata a gasar cin Kofin Ma’ajin Dutse Alhaji Babangida Umar Gantsa kuma mai neman takarar dan Majalisar Tarayya daga kananan hukumomin Birnin Kudu da Buji a zaben 2019.
Da yake jawabi a wajen bikin rufe gasar, Ma’ajin Dutse ya ce shirya gasar ba ta da alaka da siyasa, an shirya gasar ce domin sada zumunci a tsakanin kananan hukumomin biyu saboda a cusa so da kaunar juna a tsakanin matasan yankunan biyu.
A wajen gasar da aka fafata a tsakanin kungiyoyi 16 da suka fito daga yankunan kananan hukumomin biyu kulob din FC Rising Star ne ya lashe gasar da ci biyu da daya bayan ya doke kulob din FC Rangers.
Hakan ta sa FC Rising Star ya lashe kofi da kyautar Naira dubu 200 yayin da aka ba FC Rangers kyautar Naira dubu 150.
Sauran kulob 14 da suka fafata a gasar, an ba kowanensu Naira dubu 10. Ya ce zai ci gaba da gudanar da wannan gasa daga lokaci zuwa lokaci.
Da yake karin haske mai kulob din Rising Star da ya lashe gasar, Malam Ibrahim J.T ya ce gasar ta yi armashi inda ya hori ’yan kwallonsa da su ci gaba da nuna kwazo da hakan zai daukaka martabar kulob din a ciki da wajen Jihar.
An kammala gasar lami lafiya inda jama’a da dama suka yaba wa Ma’ajin Dutse game da daukar nauyin gasar musamman a tsakanin matasan jihar.