kungiyar kwallon kafa ta FC Mersel da ke Katsina ta lashe kofin Kungiyar wasan kwallon kafa ta matasa (Katsina Amateur Football Association KAFA) bayan ta samu nasara a kan Eleben Ideas da ci 1-0.
An buga wasan karshe a filin wasa da ke kofar Keke a garin Katsina a ranar Lahadin bayan an shafe wata daya ana gudanar da ita.
A lokacin rufe gasar Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar Katsina Alhaji Aminu Ibrahim Safana wanda ya samu wakilcin Daraktan Hukumar Wasanni na jiha Alhaji Nalado Ibrahim Kankiya, ya jinjina wa kungiyoyin da suka fafata a gasar, sakamakon juriya da sha’awarsu har aka kammala gasar.
Ya ce Gwamnatin Jihar Katsina ta ba bangaren wasanni muhimmanci don bunkasa rayuwar matasa a jihar, hakan ya sanya ta tura wasu ‘yan wasa Brazil don kallon yadda aka gudanar da gasar cin kofin duniya.
A karshe ya tunasar da matasa cewa za a rika tsamo ’yan wasan da ke wakiltar Jihar Katsina a manyan wasanni na kasa daga wannan gasar da KAFA ke shiryawa.
FC Mersel ta lashe kofin KAFA a Katsina
kungiyar kwallon kafa ta FC Mersel da ke Katsina ta lashe kofin Kungiyar wasan kwallon kafa ta matasa (Katsina Amateur Football Association KAFA) bayan ta…