Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, Atiku Abubakar, ya ce marigayi lauyan nan mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Gani Fawehinmi ne ya karfafa masa gwiwar bincikar ingancin takardun karatun Shugaba Bola Tinubu.
Jami’ar Jihar Chicago (CSU) da ke Amurka, ta bakin Rajistaranta, Caleb Westberg, dai ta ce takardun da Tinubu ya gabatar wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a zaben 2023, ba na makarantarsu ba ne.
- Badakalar takardun karatu: Tsohon minista ya bukaci Tinubu ya ajiye mukaminsa
- Yau sojojin Faransa za su fara ficewa daga Nijar
Westberg ya bayyana hakan ne lokacin da yake mayar da martani a kan bukatar dan takarar PDP na Shugaban Kasa a zaben da ya gabata, Atiku Abubakar ya yi, na neman a fitar masa da takardun Tinubun a can.
Atiku dai ya bukaci makarantar ta fitar masa takardun Tinubun ne saboda ya tabbatar da zargi kan badakalar karatun da yake yi masa.
Hakan dai na cikin batutuwan da ya maka Tinubu a kansu a gaban kotun sauraron kararrakin zaben Shugaban Kasa, amma ta yi watsi da su.
Sai dai duk da haka, Atiku ya ci gaba da bibiyar lamarin a gaban watan kotun Amurka a kashin kansa, wacce kuma ta ba jami’ar umarnin fitar da takardun.
Amma da yake jawabi yayin wani taron manema labarai Abuja ranar Alhamis, tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya ce bai kamata ma jami’an tsaro su dauki tsawon makonni ko ma watanni ba suna bincike kan sahihancin takardun karatun dan takara ba.
A cewar tsohon Mataimakin Shugaban Kasar, “Yanzu haka mutuncin Najeriya tangal-tangal yake yi saboda wannan batun. Ni dan kasa ne da ke kaunarta, kuma yake son ganin Dimokuradiyyarta ta inganta.
“Yanzu gaskiyar marigayi lauyan nan mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Gani Fawehinmi ta fito fili, shi ne ya fara yunkurin wannan bincike shekaru 23 da suka gabata.
“Tun a ranar 7 ga watan Oktoba ta 1999 Fawehunmi ya bukaci Babbar Kotun Jihar Legas ta sa jami’an tsaro su binciki zarge-zarge a kan Tinubu, lokacin yana Gwamnan Jihar Legas,” in ji Atiku.
Sai dai a lokacin, kotun ta ce a matsayinsa na Gwamna mai ci, Tinubu yana da rigar kariya, don haka ba za a iya tuhumarsa ba.
A yayin zaben shekara ta 1999, dai Tinubu ya yi wa INEC ikirarin cewa takardun karatunsa sun bace.