Fatima Ganduje-Ajimobi, ’yar Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano, ta shawarci matasa da su mallaki katin zaben a matsayin makamin rushe duk wata gwamnati mai gallaza wa al’umma.
’Yar Gwamnan na Kano ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram wanda take shawartar masu zanga-zangar nuna kin jinin rundunar ’yan sanda ta SARS.
- #EndSARS: ‘Ba za mu lamunci tayar da zaune tsaye da sunan zanga-zanga ba’
- Yadda zanga-zangar #EndSARS ta sa Direbobi da fasinjoji tafka asara
A sakon da ta wallafa a ranar Asabar, 17 ga watan Oktoba, Fatima ta shawarci masu kin jinin rundunar SARS kan cewa hanya daya da za su cimma burinsu ita ce mallakar katin zabe.
Ta rubuta cewa, “ku mallaki katin zabe don yin zabe kuma kada ku bar mazabar har sai an kidaya kuri’arku.”
“Ku yi raka kuri’unku har wurin tattara sakamakon zaben, ku tsaya ku jira, kuma ku tabbatar an kirga kuri’arku.”
“Matasa su ne mafi rinjaye kuma su za su ceto kasarmu Najeriya.”
Ta karkare da maudu’in kawo karshen rundunar SARS da kawo karshen zaluncin a Najeriya.
Hakazalika, mijinta Idris Ajimobi, dan tsohon gwamnan jihar Oyo, marigayi Abiola Ajimobi, ya shawarci matasa da su tabbatar sun tanadi katin zabensu don tunkarar babban zaben kasa na 2023.