✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fatima Binta Bala Ahmed: Haihuwa ba ta hana neman ilimi

Fatima Binta Bala Ahmed ita ce Uwar Soron Nasarawa, a Jihar Nasarawa, sannan Mataimakiyar Darakta a Hukumar Kula da Majalisun Tarayya da ke Abuja, ta…

Fatima Binta Bala Ahmed ita ce Uwar Soron Nasarawa, a Jihar Nasarawa, sannan Mataimakiyar Darakta a Hukumar Kula da Majalisun Tarayya da ke Abuja, ta kuma rike mukamin Babbar Jami’ar Gudanarwa a makarantar Federal Polytechnic da ke Jihar Nasarawa. Ta yi digiri na daya a kan Harsunan Najeriya  da kuma digiri na biyu a kan Huldar Jakadanci da Diflomasiyya a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Tarihin rayuwata
Sunana Fatima Binta Bala Ahmed, an fi kira na da ‘Ya Fati’. Ni ’yar gidan Sarkin Nasarawa ce. Mijina shi ne Dokta Ishak Bala Ahmed Tafidan Nasarawa. Na yi makarantar firamare ta Laranto da ke garin Jos, a Jihar Filato. Kodayake na yi makarantun firamare da yawa kafin na kammala a Laranto, saboda mahaifina ma’aikacin gwamnati ne, an rika yi masa canjin wurin aiki daga wannan gari zuwa wancan.
Na kammala Sakandaren ’Yan Mata ta Gwamnati da ke Shendam a Jihar Filato a shekarar 1980. Na yi Difloma kan Inshora a Jami’ar Ahmadu Bello a shekarar 1983, sannan na kammala digirina kan Harsunan Najeriya a Jami’ar Jos a shekarar 1988.
Bayan na kammala hidimar kasa a 1992 sai na fara aiki da Industrial Trust Fund (ITF) a Jos. Na bar wannan aikin bayan shekara 1 dalilin auren da na yi. Daga nan na fara aiki da makarantar Federal Polytechnic da ke Nasarawa, inda ta dauke ni aiki a matsayin Babbar Jami’ar Gudanarwa. Daga nan aka rika yi mini karin girma har zuwa Babbar Rijistira. Na ci gaba da aiki a makarantar har zuwa lokacin da na fara aiki da Hukumar Majalisun Tarayya da ke Abuja a shekarar 2002, inda har yanzu nake aiki da hukumar a matsayin Mataimakiyar Darakta.
Abubuwan da nake iya tunawa lokacin da nake karama
Na taso a cikin maza ne, don haka abin da maza suka yi shi nake yi. Mahaifina malamin makaranta ne kafin ya zama cikakken ma’aikacin gwamnati. Nakan iya tunawa muna takawa da kafa zuwa makaranta. Don haka duk lokacin da muka ga bishiyar mangwaro, ko dai mu hau, ko kuma mu rika jifa don mu kado mangwaron, har zuwa lokacin da masu shi za su kore mu.
Yayyena suna buga kwallo, nakan zauna in rika lura da jakankunansu. Idan aka yi kuskure littafin wani ya yage, a ranar sai na sha duka, inda zan rika kuka, sai dai kafin mu je gida za su rika roko na don in daina kuka, sannan su bukaci kada na fada wa mahaifinmu,  sun san mahaifina yana ji da ni, don haka idan ya samu labarin abin da suka yi mini za su dandana kudarsu.
Bayan mahaifinmu ya gaji da yadda muke zuwa makaranta a kafa ne, sai ya saya wa wani daga cikin yayyena keke, inda muke zuwa makaranta tare da shi, kodayake makarantunmu daban-daban, haka nake zuwa makarantarsu  Sardauna Memorial Secondary School in jira shi, bayan an tashi mu dawo gida. Wani lokaci sai na tura shi har ya fara tafiya, kafin in yi tsalle in hau.
Burina ina karama
Na so in zama Jami’ar da ke lura da fasinjojin jirgin sama, kasancewar tun ina aji 2 a firmare na hau jirgin sama zuwa Legas, don in ziyarci mahaifina lokacin da muka yi hutu, kasancewar yana aiki a can. A lokacin da muke cikin jirgi ne sai na ga yadda masu lura da fasinjoji ke yi, hakan ya ba ni sha’awa har na yi burin zama jami’ar da ke lura da fasinjojin jirgin sama.
Na fara canza ra’ayi ne lokacin da ma’aikatan banki suka rika ba ni sha’awa.
Sarautar Uwar Soron Nasarawa
Na yi matukar farin ciki da aka nada ni sarautar Uwar Soron Nasarawa, dalili kuwa shi ne, ba a taba samun mace mai wata sarauta bayan Magajiyar Gari da Madakan Kasuwa a masarautarmu ba. A lokacin da mahaifinmu ya ce yana son a samu mata masu sarauta a masarautarmu, saboda akwai wadansu ayyukan da suka shafi sarauta da mata ne za su iya yi kawai. Na ji dadin wannan nadi da aka yi mini sosai.
Nasarori
Babbar nasarar da na samu a rayuwa ita ce, ta samun ilimi mai inganci da na yi, saboda da ban yi ilimi ba, to ban san yadda zan kasance ba. Nasara ta biyu ita ce, yadda na tarbiyyantar da ’ya’yana.

Na gode wa mahaifina bisa jajircewar da ya yi har na samu ilimi, kasancewar a lokacin ba a barin mata su yi karatu bayan sakandare sai dai a yi musu aure. Duk da mun yi aure amma mahaifinmu ya ci gaba da karfafa mana gwiwar mu ci gaba da karatu, inda yake ce mana gemu ko ’ya’yana ba sa hana ilimi. Na dauki shawararsa duk da cewa bayan na kammala digirina na farko na ce ba zan ci gaba da karatu ba, ya sanya a shekarar 2008 na koma Jami’ar Ahmadu Bello don in yi digiri na biyu kan kwas din Huldar Jakadanci da Diflomasiyya. Na yi farin cikin hakan.
Farin cikin zama uwa
Na yi farin cikin zama uwa, sai dai na sha wahala kasancewar a lokacin ina zuwa makaranta, kun san yanayin zuwa makaranta da kuma lura da jariri.  Alhamdullillah a yanzu dukkan ’ya’yana sun girma.
Abin Koyi
Duk wata mace mai zurfin ilimi ina so in yi koyi da ita. Da yawansu farfesoshi ne ko kuma masu rike da manyan mukamai a kasar nan. Don haka duk lokacin da na ga wata mace da ta taka wani matsayi sai in rika sha’awarta, saboda nakan tuna kalubale da kuma wahalhalun da ta tsallake. Hakan kuma yakan sanya in jajirce wajen gudanar da ayyukana. Idan na je kauye na ga yadda sauran abokaina suke, sai in ji tausayinsu ya kama ni.
Abin da nake so a tuna ni da shi
Ina so mutane su tuna ni a matsayin wadda take taimakon jama’a, ba zan ce ina yi komai daidai ba. Na taba fada wa wata ’yar uwata da ita ma aka nada ta sarauta cewa, ya kamata mu kafa wata kungiya mai taimakon jama’a, musamman ma mata da kananan yara, mu yi abin da zai canza al’umma zuwa hanya tagari.
Hutawa da iyalina
Nakan zauna da iyalina a falo, inda muke kallon fina-finai. Ina son kallon fina-finan Hausa. Ina son tafiye-tafiye zuwa kauyuka, ban san ko don nima ’yar kauye ba ce shi ya sa haka. Idan na je mukan zauna da su mu yi wasa da dariya. Yaran yanzu ba sa son zuwa kauye.  
Darussan da na koya a rayuwa
Na koyi darussa masu yawa a rayuwa. Fuskantar kalubale na daya daga cikinsu, sannan na koyi darussa masu yawa dangane da abubuwan da suke faruwa a cikin al’umma. Na koyi darussa daga jama’ar da suke kusa da ni, sakamakon wani abu da ya faru da su.
Abin da ke sanya ni farin ciki
Nakan yi farin ciki idan jama’ar da ke kusa da ni suka kasance cikin farin ciki, ko suke cikin farin ciki sakamakon kasancewarsu tare da ni. Ina bakin cikin in ga jama’ata suna kwance ba su da lafiya. Nakan damu matuka idan na ga wani ba shi da lafiya ko da ciwon kai ne kuwa.
Nakan yi farin ciki kuma idan na ga wani yana farin ciki da abin da yake da shi duk kankantarsa. Haka nakan ji dadi idan na taimaka wa mabukata.
Yadda na hadu da mijina
Na hadu da mijina lokacin da nake makarantar sakandare. A lokacin akwai wani dan uwana, sai mahaifina ya ce masa ya ziyarce ni a ranar ziyara, bai samu damar hakan ba, sai wata rana ya zo da abokinsa, wannan abokinsa nasa shi ya zama mijina.
Babbar kyautar da mijina ya taba yi mini
Babbar kyautar da mijina ya ba ni ita ce, kyakkyawar fahimtar da ya yi mini, idan jama’a suka yi maka kyakkyawar fahimta musamman ma mijinka, to komai zai tafi sumul.
Abinci
Ina son cin tuwon dawa da miyar kuka.