Kishi kumallon mata, in ji Bahaushe, duk da wannan kirari ga mata don nuna tsananin kishinsu, an yi ittifaki cewa namiji ya fi mace zafin kishi, wanda ya sa ba a wanyewa lafiya a duk lokacin da aka ji labarin miji ya kama kwarto.
Amma sai ga shi wani abin al’ajabi wani fasto ya yi wa matar abokinsa ciki har ta haihu, kuma da cin amanar faston ta bayyana aka tunkari mijin matar, sai ya ce, wai lamarin daga ubangiji ne. Ma’ana, a wurinsa hakan babu laifi lamarin da ya ba mutane mamaki.
Wannan lamari ya faru ne a Jihar Ondo a tsakanin wani magidanci mai suna Tubosun da matarsa da Maman Precious da kuma abokinsa Fasto Akinkumi, inda Tubosun saboda amintaka ya ba Fasto Akinkumi falon gidansa a matsayin coci kasancewar ba ya da gida.
Rahotanni sun ce yayin gudanar ibada a cocin ne da mabiya ke zuwa safe da yamma da kuma tsawon zama, sai Fasto Akinkumi ya shiga masha’a da matar Tubosun wanda ganin haka ta sa yayan maigida nmai suna Moses Akinnouye ya kai ƙarar Faston ga ’yan sanda kan wuce gona-da-iri do kare mutumcin dan uuwansa.
Bayan ’yan sanda su iza ƙeyar Faston zuwa ofishinsu ne aka zo da mijin matar, maimakon ya yi ta maza ya yi abin da ya kamata, sai ya nuna hakan babu komai, duk cikin aikin hidimar ubangiji ne, hakan ya girgiza ’yan uwa da dangi da makwabtaka.
Hakan kuma ya sa abubuwan da ba a sani ba suka riƙa fitowa. Domin a cewar rahotanni bayan matar abokin Fasto ta haihu sai Faston ya kama mata gidan haya ta tare duk da tana da ’ya’ya biyu da mijinta.
Abin karin takaicin shi ne yadda aka ce Tubosun yana zuwa gidan da Faston da matarsa suke yana yi musu wanki da sauran aikce-aikacen gida.
Da aka matsa da bincike kan Fasto sai aka gano wai ya shaida wa abokinsa mijin matar ne cewa wai ubangijinsu ya aura masa matar.
’Yan uwa da dangi da makwabta sun ce wannan hali na Tubuson da walakin goro a miya.
Sun yi zargin cewa Faston ya sihirce abokinsa ne ya kwace matarsa da sunan ibada.
Sun ce idan ba sihiri ba, babu yadda za a yi Tubosun ya zama lusari ya kuma watsa wa dan uwansa ƙasa a fuska lokacin da ya kai batun ga ’yan sanda.
’Yan sanda sun bayar da belin Faston ya yi tafiyarsa gida da matar abokin. Saboda wanda yake da haƙƙi ya yi watsi da haƙƙinsa.