Wata mataimakiyar fasto mai shekara 23 ta maka faston da take matsayin na’ibarsa a kotu, inda take zargin shi da yi mata fyade sau biyu.
Mataimakiyar faston ta bayyana wa kotun yadda limamin nata, mai suna Bishop Daniel Oluwafeyiropo, ya yi mata fyade ne a lokacin da take tsaka da kallon wa’azi a talabijin a gidansa da ke unguwar Lekki a watam Yunin shekarar 2020.
- Na fi karfin kujerar Ministan Abuja a Gwamnatin Tinubu
- Yakin Sudan: Akwai yiwuwar maniyyata su kara biyan wasu kudin
An gurfanar da Bishop Daniel, wanda shi ne ya assasa cocin Reign Christian Ministry yake kuma jagorantatrsa, ne bisa tuhumar sa da aikata fyade da cin zarfi ta hanyar lalata, amma ya musanta zargin.
Mataimakiyar faston da aka sakaya sunanta, ta bayyana cewa a shekara 2018 ta fara sanin limamin cocin.
Ta ce sa fara sanin sa ne a lokacin da kawarta ta gayyace ta domin yin abada a cocin da ke yankin Akoko a Jihar Ondo, kafin daga baya ta koma mabiyar cocin, har ta samu daukaka zuwa mataimakiyar fasto.