Babbar Kotun Abuja ta dage sauraren karar da Hukumar Yaki Masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta shigar kan Sanata Shehu Sani na zargin da aka yi masa na cin hanci da damfara.
An dage shari’ar ne bayan da tafintan da ke fassarar yadda aka tattara kudin da ake zargin Shehu Sani ya karba daga Dalar Amurka zuwa Naira ya nemi bace lissafi.
- Gobara ta kone wani sashen gidan wuta na Dan-Agundi dake Kano
- Tsohon mataimakin shugaban APC ya rasu
- Wani jami’i ya kashe kansa bayan ya kasa kashe budurwarsa
Alkalin da ke sauraren karar ya ce bai gamsu da fassarar tafintan ba, kuma nan take tafintan ya ce bai da kwarewar da zai fassara canjin kudin.
Saboda haka ne alkalin ya dage zaman kotun zuwa ranar 7 ga watan Yuli tare da bayar da umurnin a samo sabon tafinta.
Kafin dage shari’ar, Alhaji Sani Dauda, wanda shi ne mai bayar da shaida a kan zargi iri biyu da ake yi wa tsohon Sanatan, ya ce ‘yan sanda sun kama shi tare da iyalansa a ranar 15 ga watan Disamba, 2019.
Shaidar Alhaji Sani Dauda
Alhaji Sani, wanda tafinta ke fassarar jawabinsa zuwa harshen Ingilishi, ya ci gaba da cewa bayan da ‘yan sanda suka sake shi, ya je ya yi masa jaje ne Shehu Sani ya je gidansa inda ya bukaci su kebe domin wata muhimmiyar magana.
Ya ce bayan sun kebe da Shehu Sani a gidansa da ke Maitama sai ya fada masa cewar sun yi maganar shari’arsa da Ministan Sharia na kasa, Abubakar Malami.
“A nan ne Shehu ya bukaci na bayar da Naira miliyan daya ga kowane daga cikin alkalai hudu da za su gudanar da shari’a ta, watau Naira miliyan hudu ke nan.
“Ya kuma ce mai gabatar da kara na hukumar EFCC ya bukaci a ba shi Naira miliyan daya, kudi suka kama Naira miliyan biyar amma na ce da shi ba ni da kudi a ranar amma ya dawo kashe gari sai na ba shi,” in ji Alhaji Sani Dauda.
Ya ci gaba da cewa ya yi kokari tsohon sanatan ya hada shi da Ministan Shari’a, amma ya ce hakan ba zai yiwu ba saboda jami’an tsaro na sa ido a kan duk wanda ke shige da fice a gidansa.
‘Ya fita da ambulan’
Ya kuma ce daga baya Shehu Sani ya kira wani mutum ta waya wanda ya kwantar masa da hankali cewar suna sane da maganarsa kuma ya yi magana da alkalan hudu da za su gudanar shari’ar.
“Sai na kira wani dan canjin kudi Abubakar na ce ya kawo mani kudi”, inji Alhaji Sani Dauda.
Bala Isma’ila, daya daga cikin ma’aikatan Alhaji Sani Dauda, ya bayyana wa kotu cewar Sanata Shehu Sani ya zo gidan maigidansa sau biyar amma bai san abin da suka tattauna ba.
Ya kuma ce ya ga Shehu Sani ya fita da wani ambulan daga gidan amma ba shi da masaniya a kan abin da ya kunsa.