Fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna 23 da ’yan bindiga suka sako sun gana da iyalai da ’yan uwansu ranar Alhamis a Asibitin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya da ke Kaduna.
A safiyar Alhamis ne iyalan fasinjojin suka yi sammako zuwa asbitin domin ganawa da su bayan wata shida a hannun ’yan ta’adda da suka yi garkuwa da su.
- Buhari ya ziyarci fasinjojin jirgin kasa a asibiti
- Ranar Juma’a kotu za ta yanke hukunci kan karar da ASUU ta daukaka
- NAJERIYA A YAU: Shin kayyade Kudaden Kamfen Zai Kawo Zabe Mai Tsafta a 2023?
Da farko fasinjojin sun gana da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wanda ya je musu dubiya a Asibitin NDA da ke Kaduna, kafin a wuce da su zuwa Asibitin Rundunar Sojin Sama inda iyalansu suka taru.
Sai dai an hana ’yan jarida samun shiga asibitin NDA inda Buhari gana da fasinjojin, haka ma an hana su shiga Asibitin Rundunar Sojin Sama, da aka mayar da su daga baya.
Sai dai Aminiya ta samu bayani daga ’yan uwan fasinjojin cewa yawancin wadanda aka sako din sun galabaita kuma suna samun kulawa a asibitin sojoin.
Duk da haka sun ki amsa sauran tamboyoyin da muka yi musu domin samun karin bayani.
A ranar Laraba ne Kwamitin Shugaban Kasa na ceto fasinjojin ya sanar ta hannun Hedikwatar Tsaro ta Najeriya cewa an sako mutanen da aka i garkuwa da su tun ranar 28 ga watan Maris, a hanyarsu ta zuwa Kaduna daga Abuja.