✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wanda aka yi garkuwa da shi ya ci zaben Majalisar Tarayya

Wanda ya ci zaben dan takarar PDP a lokacin da yake tsare a hannun ’yan bindiga ya kayar da dan majalisa mai ci

Matashin da ya ci zaben dan takarar a lokacin da ’yan bindiga suka yi garkuwa da shi, Sadiq Ango Abdullahi, ya lashe zaben dan Majalisar Tarayya.

Sadiq ya yi nasara ne bayan ya kayar da dan Majalisar Tarayya na Jam’iyyar APC na Mazabar Sabon Gari a Jihar Kaduna,  Mohammed Garba Datti, wanda ke neman tazarce.

Idan za a iya tunawa, Sadiq, wanda dan jam’iyyar adawa a PDP ne, lashe zaben fitar da gwani na jam’iyyarsa ne ne lokacin da yake tsare a hannun ’yan ta’adda da suka yi garkuwa da shi da sauran fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna.

Mahaifinsa shi ne  Farfesa Ango Abdullahi, Shugaban Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) kuma tsohon Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya.

Bayan kammala tattara sakamakon zaben, Baturen zabe na Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) na Karamar Hukumar Sabon Gari, Dokta Hashim Mohammed Sulaiman, ya ce Sadiq Ango Abdullahi na PDP ya samu kuri’a 33,616.

Na biye da shi shi ne wanda ke kan kujerar, Honorabul Mohammed Garba Datti na jami’iyyar APC, wanda ya samu kuri’a 31,737

Sauran wadanda suka kara a zaben su ne Abubakar Abdulsalam na jam’iyyar ADC da ya samu kuri’a 216, Mohammed Lawal Shehu na PRP da ke da kuri’a 222, sa’ilin da Abubakar Umar Bomo na Jam’iyyar NNPP, ya samu kuri’a 2,368.

Sauran ’yan takarar da suka sha kayi sun hada da Ismaila Mohammed na jam’iyyar NIM 125, da Lawal Ummar na Labour Party da ya sami kuri’a 8325.